TEDxZaria

TEDxZaria

Share

TEDxZaria is making history as the first TEDx event in Hausa - a language spoken by over 150 million people across Africa.

10/06/2026

Waiwaye Adon Tafiya!

Abubakar Abdulhakeem ya yi mana ɗan tsokaci game da ƙwarewar da ya samu yayin gudanar da aikin taron TEDxZaria na bara 2025

09/06/2026

Waye mutum guda da ayyukan sa/ta ke zaburar da kai kullum? Yi masa tag ka faɗi dalili.

03/06/2026

‎Me Ya Sa Za Ka Tallafa wa TEDxZaria?

‎Tallafa wa TEDxZaria ba wai kawai saka logo ko tallata suna ba ne. Dama ce ta kasancewa cikin masu gina al'umma ta hanyar ilimi, tunani, da aiki mai kyau.

‎Ta hanyar ɗaukar nauyi ko haɗin gwiwa da TEDxZaria, za ku samu damar:

‎✅ Nuna kamfani, masana'anta ko ƙungiyar ku ga ɗalibai, ƙwararrun masana, manya da ƙananan ƴan kasuwa, masu ƙirƙire-ƙirƙire, da sauran masu ruwa da tsaki.

‎✅ Nuna goyon bayan ku ga ilimi, aiyukan ƙirƙire-ƙirƙire, ci gaban matasa, da kyakkyawan tasiri ga al'umma.

‎✅ Gina alaƙa mai ƙarfi tsakanin kamfani, masana'anta ko ƙungiyar ku da al'umma.

‎✅ Haɗuwa da mutane masu basira da hangen nesa da masu kawo sauyi a fannoni daban-daban.

‎✅ Kasancewa cikin tafiyar da ke taimakawa wajen yaɗa ra'ayoyi da labarai masu amfani da kuma ƙarfafa matasa su ɗauki matakin inganta rayuwar su.

‎A TEDxZaria, mun yi imani cewa manyan sauye-sauye suna farawa ne daga ra'ayi ko tunani guda ɗaya, amma tasirin su ba shi da iyaka. Kuma suna yiwuwa ne kaɗai idan mutane da ƙungiyoyi s**a ba da goyon baya.

‎Domin ɗaukar nauyi ko haɗin gwiwa (sponsorship ko partnership), ku tuntuɓe mu ta shafin yanargizon mu ko ku turo mana da saƙo ta nan kai tsaye.

27/05/2026

🌙 Barka da Sallah!
Eid Mubarak from TEDxZaria ✨🌙

Muna yi ma dukkanin musulmin faɗin duniya Barka da Sallah, Allah Ya karɓi ibadun mu, ya sa ayyukan mu su kasance masu amfani da tasiri mai kyau a cikin al’umma. 🤍

Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization in Zaria?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address

Zaria

Opening Hours

Monday 16:00 - 20:00
Tuesday 16:00 - 20:00
Wednesday 16:00 - 20:00
Thursday 04:00 - 20:00
Friday 16:00 - 20:00
Saturday 16:00 - 20:00