Sheikh Mainasara Liman
Head preachers Fityanul Islam of Nigeria
16/03/2026
Yau kenan yayin gabatar da rufe tafsir wanda Sheikh Mainasara Liman yasaba gabatarwa wanda khalifa sayyadi Auwal sheikh Mainasara ya halinfanta.
Allah ya qara jaddada Rahma gareku maulana🤲🙏
18/02/2026
Zamani bayan zamani, azumi bayan azumi,Ni kan saurari Tafsirai daga malamai don in riƙa ƙoƙarin fahimtar abun da Allah ya aje acikin kowane malami don amfanin halittar sa.
وقَرَّبتَ للِنّاسِ وحيَ السّمَا
وسَهّلتَ صَعبا ضَربتَ مِثالا
أمَينصر هذا عطاء أتاكم
من الله في الخلق مُعطِي الجميلا.
لِحفظِ الحِمَي صِرتَ أسدَ الوغَي
بِكَرٍّ وفَرٍّ تُرِيدُ قِتَالاَ
حِمي الأوليا والنبي الهُدي
بشيخي حبيبي وجدتَ مَنالا.
Wani ya kan karantar da tafsiri don malamai su ƙara ƙwarewa.misali kamar masu fassara Jala'laini na Imam Assuyuɗi da Imam Mahalli.
Wani na karantar da shi don ya fitar da ilmomi masu zurfi acikin Addinin da rayuwar ɗan adam.
wani ya kan tafi da shi ta hanyar wa'azi da buga misalai don malami da wanda ba malami ba ya fahimci manufar Alkur'ani.
babu shakka wannan zamani sai kiran Allah ya tafi da masu buga mana misalai don kusantar da fahimtar saƙon Allah maɗaukakin Sarki.
Domin acikin harshen ɗariƙa idan kace Sheikh Ɗahiru Bauchi RTA,wanda ya kai matuƙa a wannan ɓangare,to bayan sa za ka tuna da Sheikh Mainasara Imam da wannan ƙoƙarin na kusantar da fahimta da buga misalai don fahimtar Alqur'ani mai girma.
Tafiyar zamani tana cike da tsoro, musamman idan yana tafi da masu mahimmanci acikin juyawar sa.
Allah sarki, Allah shi ne Zamani, acikin zamani mu kan tuna yarantakar mu alokacin da malam ke tafiya damu a Gwaro domin wannan Tafsir, mu kan tuna ƙurciyar mu alokacin da mu ka ga suna ɗaukar wannan Tafsiri daga a wurin Sheikh Habibullah a masallacin Juma'a,mu kanyi kukan samartakar mu alokacin da zamani ya ke raba mu da wanda mu ka saba da su.
Allah yace kui aiki mai kyau, domin yace yana gani, Manzon Allah na gani, muminai suna gani,to don haka dole a tuna abun da aka shaida.
shi yasa idan ka fara aiki mai kyau,to karka damu da wanda ya kula da wanda bai kula ba, domin mafi girman su yana sa ido akan sa.
Allah ka jiƙan su da rahama kuma kai mu su sakayya da wannan ƙoƙarin da su kai ga Wannan Addini.
Daga Alkalamin: Sayyadi Bashir
17/02/2026
Click here to claim your Sponsored Listing.