Daarus-sahaabah Network

Daarus-sahaabah Network

Share

“Doing religion best on teaching of Alqur'an and Sunna according to understanding of Prophet and his companion.”

18/06/2020

KIMIYYAR HADISI A SAUKAKE

Littafi na 1 Darasi na 11

✍️: Sheikh Muhammad Auwal Nuhu Allemawy

BABI NA BIYU:

RABE-RABEN HADISI DUBA DA INDA YA TUKE:

Bayan mun taba wani bangare na bayanan da s**a shafi sanadin hadisi kamar yadda ya gabata, na bayanin mutawatiri da Áhád, yanzu kuma za mu tsallaka mu waiwayi bangaren Matanin hadisi mu san wani abu daga siffofi da lakubbansa kafin mu dawo mu sake waiwayar sanadi da izinin Allah s.w.t.

Idan ba a manta ba a baya mun yi bayanin ma`anar matani cewa: shine abin da aka jinginawa Manzon Allah s.a.w ko waninsa, na daga zance ko aiki ko goyon bayan aikin wani.

Yanzu kuma abin da za mu sani a wannan babi da yardar Allah shine rabe-raben hadisi duba da inda mataninsa ya tuke.

Abin nufi da inda matanin hadisi ya tuke, shine wanda aka dangantawa abin da matanin hadisin ya kunsa, misali a ce Allah s.w.t ya ce kaza, ko Manzon Allah s.a.w ya ce kaza, ko sahabi wane ya ce kaza, ko tabi`i wane ya ce kaza.

Idan muka lura da wannan bayanin na karshe za mu ga cewa an danganta matanin hadisi zuwa bangarori hudu.

1- An danganta matani na farko zuwa ga Allah s.w.t kai tsaye a ka ce: Allah s.w.t ya ce kaza.
2- An danganta matani na biyu zuwa ga Manzon Allah s.a.w aka ce: Manzon Allah s.a.w ya ce kaza ko ya aikata kaza ko ya ga ana yin kaza ya goyi baya.
3- An danganta matani na uku zuwa ga sahabin Manzon Allah s.a.w aka ce sahabi wane ya ce kaza ko ya aikata kaza.
4- An danganta matani na hudu zuwa tabi`i (wanda ya ga sahabi yana mai imani kuma ya rasu bisa imani) aka ce tabi`i kaza ya ce kaza.

Duba da wadannan banbance-banbance ne malaman hadisi s**a raba mataninsa zuwa nau`o`i guda hudu, s**a kuma lakabta wa kowanne nau`i daga cikinsu sunansa da ya dace da shi.

Sunayen sune kamar haka:

- Alhadisul kudusy
(الحديث القدسي)
- Almarfu`u.
(المرفوع)
- Almaukufu
(الموقوف)
- Almakxu`u.
(المقطوع)

In sha`allahu za mu xauki wadannan nau`o`i daya bayan daya mu yi bayaninsu.

NAU`I NA FARKO: ALHADISUL KUDUSY
(الحديث القدسي)

1- Tanta

16/06/2020

Masha Allah!

Marigayi Malam Albaniy Zaria Ya Samu Jika Wadda Babban Dan Shi Abdurrahman (Abu Huraira) Tare Da Matar Shi Halima S**a Haifa. Sun Sanyawa Jaririn Suna Ibrahim.

Allah Shi Raya Ibrahim Yai Mishi Albarka Ya Dora Shi Kan Tafarkin Gwagwarmayar Yada Sunnah Wadda Kakan Shi Yayi Shahada (Insha Allah) Akai.

Want your place of worship to be the top-listed Place Of Worship in Zaria?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address

No 19 Jushin Gari
Zaria
810241