Taskar dadylasting

Taskar dadylasting

Share

Bio is loading

24/04/2026

Tamacen Kwado 🐸 Takan Wayance (Pretending) Ta Kwanta A kasa warwas t'ayi Kamar Ta mutu Don Gujewa Mating wato Saduwa Da Namijin Kwadon da bataso. Wanda be Kwanta mata a rai ba.

A Wani bincike da Masana Kimiyyar Dabbobi s**ayi,,, binciken su ya tabbatar da cewa Tamacen Kwado 🐸 jinsin European common frog,,, Suna Amfani da hikimomi Ko dabaru har salo kala (3) Don Gujewa Saduwa da Mazan Kwadi 🐸 a lokacin Breeding season Dinsu Wato lokacin da Kwadi suke saduwa Suyi Kwaï su haifi yaya a farkon damuna Kenan,,,,

A Irin Wannan Lokacin da Ake gasa tsakanin mazajen Kwadi Wajen Saduwa da Tamacen Kwadin, zaka tarar Mazan suna linka Matan yawane ,, Saboda haka pressure tana Hawa kan Matan sosai da Sosai,

Saboda haka don su huta Kokuma su Gujewa Wannan Babban alamarin da Mazan suke zuwa musu na biya musu bukatunsu .. su kuma Matan s**an kirkiri wasu dabaru kala (3) Wato three active strategic plans don Gujewa Saduwa da Mazan da basaaso Kokuma Insun gaji .

Bayaninmu zai tsallake hanyoyi biyu na farko ze Tafi izuwa ga Hanya ta (3) Domin Itace Mafi ban Mamaki daga ciki wato THANATOSIS.

THANATOSIS: Kokuma Kace tonic immobility Hanyace Wacce Matan Kwadi 🐸 suke wayancewa Dazarar sun Hango fusataccen Kwado yanufo garesu da bukatar sa, saisuyi sauri Suyi wanwar a kasa k**ar dai Yanda matacce yakeyi,

Wannan zesa Dazarar Mazan sun karaso da tsananin bukatarsu dasunga Macen a wanna yanayin jikinsu zeyi Sanyi saisuyi give up. Domin kosuma Kwadin sunsan ba'a yin tarayyar mating da matacciyar Kwado ,,, Daganan saisu hakura . Su Tafi .

Su Kuma Matan daman Likimo s**ayi . Suna Ganin Namijin ya Tafi zasuyi Tsalle su fada ruwa su Gudu Shikenan sun tsira.... Sai Wani jikon Kuma.

Wannan Hanyar tana mutukar temakawa Matan Kwadin musamman sabbin balagar cikinsu wajen kare Kansu daga injury da raunikan da gayyar fusatattun Mazan cikinsu suke yimusu Domin a wasu lokutan idan namijin Daya Yana mating da mace 1 Zakaga Sauran har compétition Sauran Kwadi na gefe suke Wajen rige rigen afkawa Macen Dazarar wancan ya gama Aiki da ITA . Daman Matan bas**ai Mazan Yawa ba . Haka akasarin ayarin Kwadi take. Mazan Sukan nunka Matan Sau k**ar 3 a Yawa. Saboda haka pressure tana Hawa kan Matan cikinsu over.

Bayan Wannan Kuma akwai wata hanyar da Matan suke Amfani da ITA wajen tarewa Saduwa da Mazan
Wato VOICE MIMICKING. suna Amfani da kwaikwayon muryar Mazan Kwadin in Wani Kwadon yataho Gurin matan, itakuma Macen Kwadob data Hangoshi zata fara kwaikwayon muryar Mazan Kwadin Wanda wannan zesa in Kwadon ya karaso hankalinsa ze rabu Gida 2. Zeke wasi wasi cewa Anya wannan ba GARDI da uwana nake kokarin haikewa ba ?? Daga karshen dai saiya hakura ya Tafi ITA Kuma Macen ta tsira kenan.

Wannann Jawabin a takaice ne. Yauwa

Doctar Zoology 🙏👋

02/02/2026

Wata rana, Hi**er ya shigo taron majalisar ministoci yana ɗauke da kaza.
Ya matse kan kazar ƙarfi a ƙarƙashin hannunsa. Yayin da yake tafiya, sai ya fara zubar mata gashi ɗaya bayan ɗaya. Kazar tana ihu da azaba, tana ta faman kuɓuta daga hannun Hi**er. Amma Hi**er bai sake ta ba, kuma bai kula da kukanta ba—ya ci gaba da zubar mata gashi kawai.
’Yan majalisar s**a ce masa:
“Kar ka azabtar da wannan talakiyar dabba haka. Ka sake ta.”
Amma Hi**er ya ƙi sauraron kowa.
A ƙarshe, bayan ya gama zubar mata dukkan gashinta, sai ya jefa kazar ƙasa. Daga nan ya fitar da ɗan hatsi daga aljihunsa, ya fara ba ta. A wannan hali, kazar—tana cikin matsanancin yunwa—ta fara kallon hannun Hi**er.
Hi**er ya kira ta ta zo kusa, yana miƙa mata hatsin. Bayan ɗan lokaci, kazar ta zo ta zauna kusa da shi, tana cin waɗancan ’yan hatsin kaɗan. Ita ce kazar da tun farko take ta faman tserewa daga hannunsa, amma yanzu ta sake komawa ta zauna kusa da shi—saboda ’yan hatsin kaɗan.
’Yan majalisar s**a tambaya cikin mamaki:
“Mene ne wannan?”
Hi**er ya amsa:
“Masu jefa ƙuri’a suna k**a da haka. Tsawon shekara huɗu da rabi, muna zubar musu da gashinsu (muna zaluntarsu). Sannan a watanni shida na ƙarshe, sai mu jefa musu ’yan hatsin kaɗan. Saboda waɗancan ’yan hatsin, masu jefa ƙuri’a s**an manta da duk zaluncin da muka yi musu tsawon shekara huɗu da rabi—sai su sake zaɓenmu.”

Darasi
Zaɓen shekarar 2027 a Nijeriya ya k**ata ya zama darasi da farkarwa ga dukkanmu.

07/01/2026

Wani saurayi yana ta kuka yana cewa duniya ta rufe masa hanya.
Yana zaune yana jiran wani ya zo ya buɗe masa ƙofa, alhali mabuɗin ƙofar yana cikin aljihunsa.

Yana ganin mutane suna wucewa suna aiki, yana cewa: “Su sun yi sa’a, ni kuma ba ni da kowa.”

Amma gaskiyar magana ita ce: bai taɓa gwada abin da yake da shi ba.

Wata rana wani tsoho ya tsaya ya ce masa: “Ba kowanne ƙofa ake buɗe ta da taimako ba. Wasu ƙofofi jarumta suke jira.”

Saurayin ya ɗauki mabuɗin, ya gwada, ƙofar ta buɗe.

A nan ne ya gane cewa babbar matsala ba rashin dama ba ce, rashin yunƙuri ne.

---

Darasi (mai ƙarfi):

👉 Kada ka jira taimako har ka manta da ƙarfinka.
👉 Abin da kake nema a waje, wata rana yana hannunka.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Ring Road
Kano
406