Info Hausa
Informations
13/05/2026
13/05/2026
Majalisar Limaman Kamaru, *CIDIMUC*, ta yi kira ga limaman masallatan ƙasar da su yi amfani da sallar Juma’a na wannan mako wajen wayar da kan al’umma kan muhimmancin zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Kiran ya zo ne a matsayin gudunmawar majalisar ga bikin haɗin kan ƙasa da ake gudanarwa kowace shekara a ranar *20 ga watan Mayu*.
A cikin sanarwar da majalisar ta fitar, ta bayyana cewa zaman lafiya ne _“gishikin rayuwa”_ da ba a iya samun ci gaba ba tare da shi ba.
Sabili da haka, ta roƙi limamai da su yi amfani da ranar Juma’a don _“karfafa zamantakewa tsakanin ƴan ƙasa, tare da tunatar da su bambancin harsuna, addinai da kabilu bai kamata ya raba mu ba.”_
Taken bikin haɗin kan ƙasa na bana shine:
*“Haɗin kan Ƙasa, Ginshikin Tsaronmu da kuma Tushen Ci Gaban Kamaru.”*
CIDIMUC ta jaddada cewa wannan taken ya yi daidai da koyarwar Musulunci wadda ke kira ga adalci, ‘yan uwanci da zaman lafiya tsakanin al’umma.
''Muna sa ran kowane limami zai sa wannan sako ya isa ga al’ummarsa. Mu yi addu’a domin Kamaru, mu yi alkawarin zama ƴan ƙasa masu karfafa hadin kai waɗanda ke gina ƙasa maimakon rushewa,”_ a cewar Dr Moussa Oumarou shugaban majalisar.
Bikin Ranar Ƙasa na 2026 zai zo ne a lokacin da ake buƙatar ƙarfafa haɗin kai fiye da kowane lokaci, domin ci gaba da tsaron ƙasa su dogara ne da haɗin kan ƴan ƙasa.
Kamaru : Tsohon shugaban majalisar dokokin kasar ya rasu bayan share shekaru kusan 40 yana jan zaren mulki a majalisar dokoki.
Tsohon shugaban majalisar dokokin Kamaru Cavayé Yeguié Djibril ya rasu yana da shekaru 86 a duniya. Mutumin da ake yi wa kallon na k*t da k*t da Paul Biya ya jagoranci majalisar dokokin Kamaru har tsawon shekaru 34, kafin daga bisani a maye gurbinsa.
06/05/2026
Shugaban majalisar limaman Kamaru CIDIMUC, Dr. Moussa Oumarou, ya gana da Nourou Dini Hassan a hedikwatar CIDIMUC a ranar Talata, 5 ga watan Mayu, 2026. Hassan dan Kamaru, ya sami karramawa a gaban duniya ta hanyar samun matsayi na biyu a gasar musabakar karatun Al-Qur'ani mai girma ta Turkiyya karo na 11. Wannan karon, Shugaban Turkiyya, mai girma Recep Tayyip Erdoğan, ya mika masa kyautarsa tare da taya shi murna da yi masa fatan alheri.
04/05/2026
Gwamnatin Kamaru ta sanar a hukumance cewa kamfanin da ke oula da wutar lantarki a kasar ya sauya suna daga Eneo Cameroun S.A. zuwa Société Camerounaise d'Elecitricité SOCADEL,
biyo bayan kammala yarjejeniyar sake fasalin tsarin samar da wuta.
Mai sauya sunan zai canza a rayuwar yan Kamaru?
Cliquez ici pour réclamer votre Listage Commercial.
Type
Site Web
Adresse
New Bell
Douala