Pharmactivity

Pharmactivity

Share

Mu tattauna akan magunguna da kuke sha!

15/05/2026

Shawara,

Kada kabari wani ya rude ka kana AS ko SS ya gayamaka cewa zaka iya auren AS irin ka ko SS akan cewar ai anayin dashen 'bargo.

Dashen 'bargo yana da tsada sosai, ba kowa bane ke iya biya ayi masa ba. Bama wannan ba, ko anyi dashen 'bargon, har wa yau wa jiya yanyanka zasu iya gadon cutar amosanin jini.

Maganar kuma ana iya canza jinsi (genotype) wannan zance qarya ne. Tatsuniya ce kawai.

Mu kiyaye.

03/04/2026

Akwai karuwar cutar koda sosai a yankin Arewa maso Gabashin k'asar nan. Rahotanni sun nuna cewa mutum 1 cikin kowane 30 na fama da ita.

A cikin ‘yan watannin baya, jihar Yobe na fuskantar wannan matsala, kuma Yobe na d'aya daga cikin jihohin Arewa maso Gabas.

Ana iya kare kai daga cutar koda.

A rik'a shan ruwa da yawa, a guji amfani da magunguna ba bisa k'a’ida ba (musamman magungunan rage zafi), sannan a rik'a motsa jiki akai-akai.

Want your business to be the top-listed Health & Beauty Business in Lucknow?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Address


Lucknow
226026