Arewa post 24

Arewa post 24

Condividi

Arewa post for all

10/07/2026

🇮🇷 Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da nuna girmamawa ga babban jagoran mabiya Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky.

A tsawon shekaru, jami'an gwamnatin Iran sun sha bayyana goyon baya da damuwarsu game da halin Sheikh El-Zakzaky, tare da kira da a ba shi kulawar lafiya da kuma mutunta haƙƙoƙinsa. Haka kuma, a lokuta daban-daban, Sheikh El-Zakzaky ya kai ziyara Iran inda aka tarbe shi da girmamawa daga jami'ai da mabiyansa.

08/07/2026

Da ɗumi-ɗumi: Matashi Mafi Ƙarancin Shekaru Hon Zaharadden A Zangina Ya Karɓi Takardar zama halastaccen ɗan Takarar Majalisar Tarayya a Jam'iyyar NDC.

Hon. Zaharadden A. Zangina ya karɓi takardar shaidar zama cikakken ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Karu, Keffi da Kokona na Jihar Nasarawa a ƙarƙashin jam'iyyar NDC.

Zaharadden ya kafa tarihi kasancewar shi ne mafi ƙarancin shekaru a cikin dukkan 'yan takarar da ke neman kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya a Najeriya, lamarin da ya jawo hankalin masu bibiyar siyasa da matasa a faɗin ƙasar.

Masu goyon bayansa sun bayyana karɓar takardar a matsayin wani sabon babi na siyasar matasa, tare da nuna ƙwarin gwiwar cewa zai kawo wakilci nagari da sabbin dabaru idan ya samu nasara a zaɓen da ke tafe na 2027

08/07/2026

𝗠𝗘 𝗬𝗔 𝗦𝗔 𝗬𝗔 𝗦𝗔𝗠𝗨 𝗞𝗔𝗙𝗔 𝗛𝗨𝗞𝗨𝗠𝗔𝗥 '𝗣𝗥𝗘𝗦𝗜𝗗𝗘𝗡𝗧𝗜𝗔𝗟 𝗙𝗢𝗥𝗘𝗜𝗚𝗡 𝗜𝗡𝗧𝗘𝗥𝗩𝗘𝗡𝗧𝗜𝗢𝗡 𝗣𝗥𝗢𝗠𝗢𝗧𝗜𝗢𝗡 𝗖𝗢𝗨𝗡𝗖𝗜𝗟' — DG

Babban Daraktan hukumar da ake zargi da kasancewa ba ta halastacciya ba, Adeniyi Adeyemi Matthew, ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya ƙirƙiri abin da ya kira Presidential Foreign Intervention Promotion Council shi ne domin inganta haɗin gwiwar Najeriya da ƙasashen waje da kuma jawo zuba jari.

Sai dai hukumomi sun bayyana cewa wannan hukuma ba ta cikin hukumomin gwamnatin tarayya da doka ta amince da su, lamarin da ya sa aka dakatar da ayyukanta, yayin da ake ci gaba da bincike kan zarge-zargen da s**a shafe ta.

08/07/2026

KAJI SHUGABA MAI ADALCI;-

Duk da cewa shi har yanzu Kyaftin ne, Ibrahim Traoré ya ƙara wa jami'an soja uku girma zuwa mukamin Janar a Burkina Faso.

08/07/2026

ICPC TA HANA EL-RUFAI JINYA, TA K**A LIKITANSA – ADC TA ZARGI GWAMNATIN TINUBU DA TSANANTA MUSUN ZALUNCI

Jam'iyyar ADC ta yi zargin cewa jami'an ICPC sun hana tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufai, samun kulawar lafiya a Asibitin Ƙasa da ke Abuja duk da shawarar likitoci cewa a kwantar da shi saboda halin da lafiyarsa ke ciki. Ta kuma yi zargin cewa an ci zarafin matarsa tare da k**a likitansa yayin da suke ƙoƙarin ganin ya samu kulawa.

A cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai na ADC, Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, jam'iyyar ta ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na amfani da hukumomin gwamnati wajen muzgunawa 'yan adawa, tana mai kiran El-Rufai da "fursunan siyasa". Ta buƙaci a ba shi damar ganin iyalansa, lauyoyinsa da likitocinsa ba tare da takura ba, tare da sake duba sharudan belinsa.

Sai dai ICPC ta ce ta k**a likitan El-Rufai ne saboda zargin karya da kuma take umarnin kotu yayin ziyarar asibitin, inda ta musanta zargin da ake yi mata.

Vuoi che la tua azienda sia il Società Di Media più quotato a Verona?
Clicca qui per richiedere la tua inserzione sponsorizzata.

Sito Web

Indirizzo


Verona