Arewa Reporters 24
Shafi ne da ya himmatu wajen kawo labarai na gaskiya tare da sharhi akan al'amuran siyasar Najeriya na yau da kullum. Harma Nishadi
05/12/2023
Kungiyar Izala Ta Yi Allah Wadai Da Ķìśan Kiyashin Da Sojoji S**a Yi Wa Musulmai A Kaduna
Kungiyar wa’azin musulunci ta Izala tayi Allah wadai da kisan kiyashi na harin wani jirgin sama da aka yiwa al’ummar musulmai a jahar kaduna yayin da suke gudanar da wani taro.
Shugaban kungiyar Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, yayi kira ga gwamnantin tarayya da tayi bincike na gaskiya Akan hakikanin abun da ya faru, kuma ta hukunta masu hannu a cikin wannan lamari.
Lamarin de ya faru ne a kauyen Tudun Biri da ke gundumar Afaka a lardin Rigasa a karamar hukumar Igabi, inda aka yi kuskuren kashe musulman da suke gudanar da wani taro tare da jikkata wasu da dama biyo bayan wani hari da jirgin yaki mara matuki na soja ya kai don farautan ‘yan ta’ada.
Sheikh Bala Lau yayi jimami kwarai, ganin yadda daruruwan mutane s**a rasa ransu a wannan lamari. A karshe yayi addu’ar Allah ya Jikan musulmai muminai, ya baiwa wadanda s**a ji rauni lafiya, ya kuma kiyaye faruwar haka a gaba.
JIBWIS NIGERIA
MANYAN LIKITOCIN DUNIYA GUDA 11 NE
1. Alqur'ani Mai Girma
2. Yawan shan ruwa
3. Bacci wadatacce da daddare
4. Iska mai kyau
5. Tafiyar rabin awa a kasa kullun
6. Abinci mai gina jiki madaidaici
7. Hasken rana
8. Zuma
9. Habbatus Saudah
10. Yarda da kaddara mai kyau koh maras kyau
11. Furta "Laa'ilaaha illallah"
KARIN BAYANI
Idan kayi zargin kanka kace astaga furula
Idan kaji radadi "Alhamdulillahi"
Idan abu yabaka mamaki "Subhaanallah"
Idan kana cikin farin ciki "Salatin Annabi ﷺ"
Idan kana cikin bakin ciki "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"
Idan kaga abun mai ban sha awa kace "Mashaa Allah Tabarakallah"
Ka fara komai da "Bismillahi"
Ka rufe komai da "Alhamdulillahi"
Ina rokon Allah Ya yarda da ni da ku babu komai bayan yardar Sa sai Aljannah In shaa Allahu...
*Kada ka/ki Wuce Baka turawa jama'a ba. Allah Ya sa muna daga cikin masu samun babban rabo ranar gobe kiyama, aameen Ya ALLAHU.*
Assalamu Alaikum Masoya Kasar Nigeria 🇳🇬 Dama Arewa Reporters 24.
Muna yawan Samun Sakon Al'umma Cewa Suna Turo Sakonninsu A Wannan Shafin Mai Albarka, Kuma Sunason A 'Daura Amma Ba'a 'Daurawa.
Maganar Gaskiya Bawai Bama Son 'Daurawa Bane, Amma idan Mutun Yanason A 'Daura Sakon shi A Wannan Shafin a Arewa Reporters 24 .
Ga Yanda Mutun Zai Turo Sakon shi a Wannan Shafin Shine Katuru Sako Ta Massage, Amma Kasan idan zaka Turo Sakon Na Gaskiya ne.
Idan kuma Sakon Yashafe Fadakarwane ko Nishadantarwa ne Banda Cin Mutunci Wani Mutun ko Wani Addini Ko Cin Zarafin Wata 'Kabila ko Wata Kasa.
Haka Zalika Banda Kwafan Wata Shafin Batare da Izinin Wannan Shafin Ba.
A Tabbatar Ambi Doka, Domin Zama Daya Daga Cikin Masu Jagoranci a Wannan Shafi ta Arewa Reporters 24
Muhammad Rasulullah
Sallu Alaihi wasallam
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Abuja
AREWAREPORTERS24