A R N Hausa

A R N Hausa

Share

A R N jarida ce da take yaɗa labarai da rahotanni gami da muhimman bayanan da s**a shafi nahiyar Africa.

27/11/2025

Rasuwar Sheikh Usman Ɗahiru Bauchi: Shaikh Ibraheem Zakzaky Ya Miƙa Ta'aziyya

Duniya ta yi jimami kan rasuwar babban malami Sheikh Usman Ɗahiru Bauchi (R), wanda ya rasu a yau, 06/Jimada 11/1447. Sheikh Bauchi ya kasance daya daga cikin fitattun malamai da dalibai da malamai da dama s**a amfana da iliminsa.

Jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya mika sakon ta’aziyya ga iyalai da ɗaliban marigayin, yana mai roƙon Allah Ya saukar da rahamarsa, Ya sanya aljanna ta zama makomarsa, sannan Ya ba wa iyalansa da masoya haƙuri da juriyar wannan babban rashi.

Masoya da mabiyan Sheikh Bauchi sun nuna alhini kan rasuwar wannan babban malami, wanda ya yi fice wajen ilmantar da al’umma da tafiyar da harkokin addini.

A R N Hausa

26/11/2025

Ƴan uwa Musulmi, almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), sun gudanar da gangamin nuna adawa da yunkurin Amurka na rura wutar matsalar tsaro a Najeriya. Gangamin ya gudana a bakin ofishin Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Kasa, dake Maitama, babban birnin tarayya Abuja. Masu zanga-zangar sun dauki wannan mataki ne domin bayyana rashin amincewarsu da tasirin kasashen waje kan harkokin tsaro a Najeriya.

A R N Hausa

Want your business to be the top-listed Media Company in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Abuja