Count The Clock Reporters
Revolutionary, struggle, fighting against injustice
15/02/2022
Jihohin Najeriya da dama sun shiga wannan makon da matsananciyar matsalar man fetur, wadda daman tun bayan sati biyu da s**a gabata kasar ke cikin wannan matsala.
Bayan kwanaki da fara fuskantar ƙarancin man sai kuma aka fara samun wani gurbataccen man fetur wanda ya ringa lalata abubuwan hawa.
A dalilin samun wannan matsala hukumomi s**a bayar da umarnin dakatar da sayar da man , har ma shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin cewa lallai sai waɗanda s**a shigar da man kasar sun yi bayani, yana mai bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare 'yan kasar daga duk wani abu da za a samar wanda zai cutar da su.
Wannan matsala ta karancin man dai ana ganin ta haifar da gagarumin koma-baya ga harkokin tattalin arzki na jama'a da ma gwamnati kuma za ta ci gaba da hakan har zuwa lokacin da za a shawo kanta.
Shin me zakuce gameda da wannN hali da Najeria ta samu kanta?
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Abuja