Arewa Rest Tech

Arewa Rest Tech

Share

Arewa Rest Tech is a group of intellectual and young men from far Northerner to tech all tech issues.

09/02/2023

Define of social media and that you should explain "is social media a science or an art".

Ans

Social media refers to a group of internet-based applications that allow individuals and organizations to create, share, or exchange information, ideas, and content in virtual communities and networks. Examples of social media include Facebook, Instagram, Twitter, LinkedIn, and many others.

As for whether social media is a science or an art, it can be argued that it encompasses elements of both. On the one hand, social media has a scientific aspect in that it involves the collection and analysis of data, as well as the use of algorithms and other technical tools to reach specific objectives. On the other hand, social media also requires creativity, intuition, and the ability to effectively engage and connect with audiences, which are more artistic qualities.

Ultimately, the answer to whether social media is a science or an art depends on how it is used and the context in which it is being discussed. But, in my opinion, it is a combination of both science and art. Social media requires both a technical understanding of how it works and the ability to use that understanding to create compelling and effective content that resonates with your target audience.

Copied

14/10/2022

🔰AREWA REST-TECH🔰

GARAƁASA ZUWA GA 'YAN AREWA

Garaɓasar ga masu sha'awan koyan Crypto, Forex, Digital Marketing da sauran Fasahar Zamani na yanar gizo....na bada irin wannan Garaɓasar ƙwanaki har na raba PDFs guda 10 na waɗanda na rubuta da waɗanda nima nasiya da kuɗina a wani a group da na samar akan naira dubu ɗaya kacal.

Yanzun na sake buɗe Sabon Group ga masu niyya sai ku mun magana ta wannan number
08142677179 domin kasancewa a wannan babban Garaɓasar dana bude akan Naira Dubu Ɗaya Kacal.

A cikin PDFs akwai wanda na siya guda daya ya kai Naira Duba Goes (10k) da sauran manyan littafai daga Hausa zuwa ga turanci dukka zan bada su akan naira dubu ɗaya kacal.

PDFs ɗin sun haɗa da littafina na Cikakkiyar ilimi akan Forex Trading, Cryptocurrency, ilimin kariya da yake koyar da ilimin tsaron na'ura da bin diddigi da sauransu, da kuma littafin koyon kasuwancin Online wanda nayi bayanin hanyoyin kasuwannin Online guda 11 wanda guda ɗaya idan ka ɗauka a ciki zaka dinga samun kuɗi dashi a Online, da sauran takardu masu muhimmanci da na rubuta.

Bayan rufewar sai wasu da basu samar damar shiga cikin Group na garaɓasar ba s**a dinga min magana akan sunason shiga domin mallakar waɗannan takardu na Blockchain Technology, Cyber Security, Ethical Hac-king, Networking da sauransu.

Bayan nan naga ya dace in sake sabon Garaɓasar shine naga yiyuwar sake sabon Garaɓasar ga mutanen Arewa saboda muma mu morin wannan Fasahar Zamani. Yanzu nayi tunanin baku dama daga yanzu zuwa gobe da misalin karfe 11:00am na safe, duk mai son shiga zai iya yayi mana magana ta WhatsApp: 08142677179 ya biya dubu ɗaya ya shiga cikin group ɗin, idan mutane s**a kai mutum 100 a gaskiya mun rufe kenan.

Ko kuma kabi ta wannan link din
👇 👇 👇
https://wa.link/7ebf5n.

Allah Ya taimakemu gaba daya.
Ameeeeen🙏

11/10/2022

ZAKA SAMU ƘYAUTAR DALA BIYU $2 (₦1,200) IDAN KAYI REGISTER DA MARA WALLET.

Duk Mutum Ɗaya Idan Kagayyato Zasu baka Dala Ɗaya $1 (₦600)🤑

Mara Sabuwar Exchange-ce Wacce Zata fara Aiki Nan kusa Bada jimawaba.

A yanzu haka idan kayi register Zasu baka $2 sannan Duk Mutum ɗaya idan kagayyato musu zasu baka $1

Ga Link ɗin da zaka shiga kayi Register:

https://mara.xyz/me/JAF600

Idan ka shiga Linkɗin zaikaika inda zaka saka Email address ɗinka Zaka ga "Sign-up" Saika Latsa
Bayan Kayi Sign-up Zaka ga Tambarin
-Google Play
-App Store
Idan Wayarka Android-ce Sai kashiga Google Play Kayi Install ɗin Mara Wallet.

Daga nan Sai kaje Kaduba Gmail ɗinka Zakaga Sun turama da Verification Link a Gmail ɗinka Sai kaje ka latsa inda akasa "Verify Your Email" Zasuyi Verify na Email ɗinka daga nan kuma Sai ka ƙarasa Cike sauran informations ɗinka.

✔️ First Name:
✔️ Surname:
✔️ Phone Number:

Sai kayi Clicking Zasu kaika inda zaka saka OTP Code Zasu turoma da Code ɗin a Lambar dakayi Register da'ita Sai kayi Copyn Code ɗin kasaka Shikenan Kagama.

Sai kaje Cikin App ɗin Kayi Login

Dazarar ka kammala Register zasu baka dala biyunka. Kaima zaka'iya Copy Referral Link ɗinka katurama Abokanka Duk mutum ɗaya idan yayi Register da Link ɗinka kanada dala $1
Ka hanzarta Kayi Register Kasamu Rabonka Kafin Sudaina Bayarwa
https://mara.xyz/me/JAF600

Photos from Arewa Rest Tech's post 26/09/2022

🔰AREWA REST-TECH CRYPTO🔰

BABI NA ƘARSHE AKAN KUƊI

SIFFOFIN DA YANAYIN KUƊI

Akwai siffofi da ɗabi'un nagarta da ya kamata duk wani abu da a ke amfani da shi a matsayin kuɗi ya kasance yana da su. Mafi yawan abubuwan da mutane s**a dinga amfani da su a matsayin kuɗi ba su gama cika ingantattu ba, saboda ba su gama haɗa dukkanin siffofin ba.
Kuɗi mai cikakken inganci shi ne wanda ya haɗa halayen nan guda shida:

1. Durable

2. Divisible

3. Transportable

4. Non-counterfeit able

5. Valuable

6. Generally accepted

1. Durable: Duk abin da za a yi amfani da shi a matsayin kuɗi ya kyautu abin ya kasance yana da; ƙarkon jimawa ta yadda za a iya adana shi na tsawon lokaci ba tare da ya lalace ba, komai tsawon lokacin da a ke amfani da shi ba zai koɗe ba, kalar jikinsa ba za ta canja ba, idan fari ne zai tabbata a matsayin farin ba zai koma wata kalar ba, idan an ajiye shi komai tsawon lokaci girman jikinsa da kaurinsa ba zai ragu ba, sannan yanayin zafi ko yanayin sanyi ba za su sanya ya ruɓe ko ya lalace ba. Bisa la'akari da haka za mu iya ganin da yawa daga cikin nau'ikan kuɗaɗen da al'umma daban-daban s**a yi amfani da su ba kowanne ne ya ke da ƙarkon da a ke buƙata ba, hatta kuɗaɗenmu na takardu ba su da ƙarkon jimawa sosai, saboda suna iya lalacewa ko su koɗe ko kuma su yayyage ya kasance sun yi lalacewar da ba za a karɓa ba sai dai a ƙona. Bai kamata kuma a ce kuɗaɗe za su iya lalacewa ta yadda mai su zai yi asara ba, kamata ya yi nagartarsu ta tabbata yadda mai su ba zai yi asara don ya ajiye su na tsawon lokaci ba. Amma zinare a matsayin kuɗi idan muka duba za mu ga yana da ƙarkon
da a ke buƙata; kalarsa ba ta koɗewa, adadinsa ba ya raguwa, ba ya lalacewa ballantana wanda ke da shi ya zam ya yi asara, komai tsawon
shekaru idan ka ajiye shi za ka same shi yana nan yadda ka ajiye shi.

Haka su ma kuɗaɗen digital kasancewar su lambobi to su ma ba sa lalacewa kuma ba sa koɗewa ko raguwa. Sai dai su kuɗaɗen digital da ya ke su nau'in kuɗin fiat ne da Gwamnati ke samarwa, ƙarkonsu ya ta'allaƙa ne da Gwamnati domin duk da ba sa lalacewa amma idan Gwamnati ta ce a daina karɓar su to sun tashi a matsayin kuɗi sun zama lambobin da ba su da bambanci da lambobin cikin calculator.

2. Divisible: Hali na biyu da ya kamata kuɗaɗe su kasance suna da su: su zama masu sauƙin rarrabawa ta yadda za a iya amfani da su a sayi manyan kayayyaki da ƙananun kayayyaki. Amma idan ya kasance ba za a iya amfani da su a sayi ƙananun abubuwa ba sai dai manya, to ba su gama cika siffofin da za a iya kiransu da kuɗaɗe ingantattu ba. A wannan fannin idan muka duba za mu ga abubuwa da yawa da aka yi amfani da su a matsayin kuɗi kamar; gishiri, sulallan zinare, kuɗaɗen takarda dama kuɗaɗen lambobi, dukkaninsu ana iya amfani da su a sayi manyan kayayyaki har ma da ƙananu.

3. Transportable: Kafin kuɗaɗe su gama cika ingantattu, dole sai idan ana iya ɗaukar su a
yi tafiya da su daga wani guri zuwa wani guri ba tare da an sha wahala sosai ba. Amma idan ya kasance kuɗaɗe ba za ka iya ɗaukar su ta daɗi ka tafi da su kasuwa ka yi sayayya ba, to suna da rauni ta fuskar inganci.

A wannan ma idan muka duba za mu ga abubuwa da yawa da aka yi amfani da su a matsayin kuɗi yawancin su ana iya ɗaukar su ayi zirgazirga da su ta daɗi, sai dai wasu sun fi wasu sauƙin zirga zirga-zirgar. Misali, kuɗaɗen zinare sun fi gishiri, fata da makamai sauƙin ɗauka a yi zirga-zirga da su, yayin da su kuma kuɗaɗen takarda sun fi na zinare sauƙin ɗauka da zagayawa duk inda a ke so, kuɗaɗen digital na lambobi kuma sun fi kuɗaɗen takarda sauƙin ɗauka domin a cikin wayarka sai ka ɗauki adadin kuɗaɗen da sai an cika babbar mota da kuɗaɗen takarda ba a iya ɗauke su ba.

4. Non-counterfeitable: Kafin kuɗi ya zama mai nagarta sai idan yana da wahalar kwaikwaya ta yadda mutane ba za su iya yin jabun su ba, saboda idan ya kasance kuɗaɗe suna da sauƙin bugawa to zai zama ba su da daraja ta yadda mutane da yawa za su zaɓi su buga kuɗin maimakon sarrafa kayan da za su sayar su samu kuɗin. A wannan ma idan mu ka duba za mu ga; gishiri, fata, tagulla, tasa da zinare dukkanin su suna da wahalar kwaikwaya ko ma ba za a iya kwaikwayon su ba. Su ma kuɗaɗen takarda suna da wahalar kwaikwaya sakamakon Gwamnati ta keɓe nau'in takarda da tawadar zana su ta yadda za su yi wahalar mallaka ballantana a buga kuɗi da su, duk da a kan samu lokuta da yawa wasu su iya buga jabunsu kuma ya zamanto mutane suna kashe su ba tare da sun iya bambanta jabun da na ainihi ba. Su ma kuɗaɗen digital a nasu ɓangaren suna da wahalar kwaikwaya sakamakon ikon samar da su yana hannun Gwamnati ne ita kaɗai.

5. Valuable: Masana s**a ƙara da cewa, kuɗaɗe ba sa zama cikakkun ingantattu idan
ba su zama suna da daraja a karan-kansu ba. Duk abin da da za a yi amfani da shi a matsayin kuɗi ya dace ya zamto yana da ƙima ta yadda ko da an daina amfani da shi masu shi ba za su yi asara ba, domin za su iya amfani da shi su sarrafa kayan biyan buƙata da za su iya sayarwa a ba su kalar kuɗin da aka koma ana amfani da su. Amma idan ya kasance kuɗaɗe ba su da wata daraja a karan kansu ta yadda idan aka daina amfani da su mai su ba zai iya sarrafa su ba sai dai ya watsar to ba su gama cika masu inganci ba. A wannan fannin ma idan muka duba za mu ga yawancin abubuwan da aka yi amfani da su a matsayin kuɗi suna da amfani don ko da ma ba a ba su matsayin kuɗi ba mutune na amfani da su kamar; gishiri, ƙarafuna, makamai, fata da zinare. Amma kuɗaɗen takarda da kuɗaɗen digital
dukkanin su ba su da wata daraja ko amfani, idan aka daina amfani da su ita kanta Gwamnati ƙona su ta ke yi saboda rashin amfanin su. Darajar kuɗaɗen takarda da na digital daraja ce ta doka, Gwamnati ta zartar cewa a dinga karɓar su saboda haka mutane su ke karɓar su ba don suna da wata daraja ba. Sai dai wasu daga cikin masana kuma suna ganin duk da kuɗaɗen Gwamnati ba su da wani amfani ko daraja a karan kansu, amma wahalar kwaikwaya da su ke da su shi ma daraja ne, don idan ya kasance ba za ka iya samar da abu ba kuma kana buƙatarsa, idan kana son mallakarsa sai ka yi aiki tuƙuru kafin ka samu, to iya wannan ma daraja ne. Koma dai ya ya, suna da darajar ne saboda Gwamnati ta zartar da dokar a ke ƙarbar su, idan gobe ta ce a daina amfani da su to sun zama abin da Hausawa ke kira da "Fasassar ƙota ba ta moriya sai jifa."

6. Generally Acceptability: Abu na ƙarshe kuma mai mahimmanci da ya kamata kowanne kuɗi ya zama yana da shi, shi ne ya zama ilahirin al'umma suna karɓar sa a matsayin kuɗi. Amma idan ya kasance kuɗi ba a ko ina za ka je ka ba da su a karɓa ba, to ba su gama zama masu inganci ba. A wannan fannin ma idan muka duba za mu ga abubuwa da yawa da aka yi amfani da su a matsayin kuɗi a zamaninsu ana karɓar su a kusan ko a ina, kamar zinare da a zamanin da a ke amfani da shi a matsayin kuɗi babu yankin da za ka je ka ba da shi ba a karɓa ba, saɓanin kuɗaɗen Gwamnati wanda a ke karɓa a iya ƙasar da a ke sarrafa su kaɗai. Duk da ya ke kamar Naira duk inda ka je a faɗin Nijeriya ka miƙa ta za a karɓa a ba ka abin da ka ke buƙata, amma a wasu ƙasashen ba za a karɓa ba. Dalilin da ya sa a ke iya karɓar zinare a ko ina cikin faɗin duniya a zamanin da a ke amfani da shi a matsayin kuɗi shi ne, saboda al'umma ne s**a haɗu wajen yarda da shi a matsayin kuɗinsu ba ƙaƙaba masu shi aka yi ba, sannan kowa na iya haƙo shi gwargwadon adadin da zai iya, ba kamar kuɗin Gwamnati da ita kaɗai ce ke da ikon samarwa ba.

Wannan shine karshen darasin mu akan kuɗi. Allah yasa mudace. Ameeeeen ya Allah

Ina tare da Financial Analyst Avokina Comrafe Mubarak Badamasi Babangida

https://www.facebook.com/profile.php?id=100086001708799

Want your business to be the top-listed Computer & Electronics Service in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Abuja
900001