Ibn Taheer

Ibn Taheer

Share

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيم

Photos from Ibn Taheer's post 11/12/2025

Muzaharar Maulidin Sayyida Zahra (S), Daga Abuja

Harkar Musulunci karkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H), ta gudanar da gagarumin muzaharar Maulidin Sayyida Zahra (S), a Abuja

Muzaharar wacce aka farota tun daga gudu Market, har zuwa gudu junction dake cikin Apo cikin birnin tarayya, Matasa da sauran al'ummar sun halarci muzaharar, ta gudana kuma cikin izza.

Anyi lafiya an tashi lafiya.

Isa Charis
AliAssajjad Ibn Taheer
11th/ Dec/ 2025

Photos from Ibn Taheer's post 10/12/2025

MAKON SAYYIDA ZAHRA (S) RANA TA (2) A ABUJA

Sisters forum na Harkar Musulunci karkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H), ta cigaba da gudanar da Taron Maulidin Sayyida Fateema (S) a Abuja

Makon wannan shekarar wanda ya dauki sabon salo, an fara da bude taro da addu'a, daga bisani aka gudanar da takaitaccen Majalisin Mawaka, sannan aka shiga jawabai, inda aka tattauna kan rayuwar Sayyida Zahra (S), wanda sister forum s**a gabatar, tare da koyi da zamantakewar Sayyida Zahra (S) din.

Bayan idar da salloli, an dawo zango na biyu, wanda Malamai mabanbanta s**a tattauna akan Sayyida Zahra (S), su Sheikh Abbare s**a fara da bayani akan jarumtar Sayyida, tare da Dr Shamsu Zuru s**a gabatar da jawabi na gaba, daga karshe Sheikh Salihu Ahmad Lazare ya gabatar da jawabi na karshe, sannan aka cigaba da majalisi tare da cin abinci.

Daga bisani an rufe taro da addu'a, tare da addu'ar Allah yakai kowa gida lafiya" gobe za'a cigaba da gudanar da taro.

Isa Charis
AliAssajjad Ibn Taheer
10th/ Dec/ 2025

05/12/2025

Wakar waki'ar Buhari

Want your business to be the top-listed Media Company in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Abuja