Manara RADIO
Radio channel that sheds light to listeners in Africa,Middle East and across the globe, predominantly "HAUSA" on Islamic tenets and civilization
LABARUN DUNIYA
SHUGABA TINUBU YA NUNA JUYAYIN LABARIN KISAN GILLA GA DAYA DAGA MALAMAI DA A KA SACE A JIHAR OYO
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nuna matukar juyayin labarin kisan gilla ga daya daga malaman da a ka sace a makarantar Grammar ta Baptist da ke karamar hukumar Orire a jihar Oyo.
Rahotanni sun bayyana masu satar mutane sun sace malamai da daliban a makarantar ta al’ummar Esiele a karamar hukumar Orire.
Shugaba Tinubu ya ce babban sufeton ‘yan sanda na jagorantar ceto wadanda a ka sace, inda ya yi amfani da sakon wajen jajantawa gwamna Seyi Makinde da al’ummar Oyo kan wannan akasin.
Kazalika shugaba Tinubu ya nuna wannan na nuna lokaci ya yi da za a kafa rundunar ‘yan sandan jiha.
Shugaban ya bukaci majalisar dokoki ta gaggauta yin doka don kafa rundunar ‘yan sandan jiha da hakan zai taimaka wajen kula da yankunan da ba su da wadatar jami’an tsaro.
Yayin da gwamnatin tarayya da gwamnoni da dama ke mara baya ga kafa rundunar ‘yan sandan jiha, wasu masu sharhi na nuna fargaba ‘yan siyasa ka iya juya lamarin ‘yan sandan zuwa ‘yan kanzaginsu.
RUNDUNAR SOJAN NAJERIYA DA HADIN GUIWAR AMURKA SUN KAI FARMAKI KAN ‘YAN ISWAP
Rundunar sojan Najeriya da hadin guiwar rundunar sojan Amurka ta Afurka sun kai farmaki ta samaniya kan ‘yan ta’addan ISWAP a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
Hare-haren k**ar yadda sanarwa daga daraktan labaru na rundunar tsaron Najeriya Manjo Janar Samaila Uba ta bayyana cewa farmakin ya hallaka jigogin ta’addan ISWAP 20.
A cikin harin dai har da labarin kashe kwamandan ISWAP Abu Bilal Al-Manuki wanda ba mamaki wani mai k**a da sunansa ne a ka ba da rahoton kashewa a can baya.
Manjo Janar Uba ya ba da tabbacin cigaba da hare-hare don kore duk ‘yan ta’adda su rasa mafaka a yankin kasar Najeriya.
In za a tuna rundunar sojan Najeriya ko gwamnatin Najeriya ta ba da labarin hadin guiwa da sojan Amurka inda akalla sojojin Amurka 100 su ka sauka a Najeriya ta birnin Bauchi.
TSOHON GWAMNA ELRUFAI YA KI FITA DAGA MOTA LOKACIN DA A KA GARZAYA DA SHI OFISHIN DSS
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasiru Elrufai ya ki amincewa ya fito daga mota lokacin da a ka garzaya da shi ofishin rundunar tsaron farin kaya DSS.
Wannan dai ya biyo bayan samun beli da ya yi amma da sharudda masu tsauri da su ka hada da mika fasfo dinsa da kuma zuwa kai kansa ofishin DSS duk Jumma’a har a kammala shari’a.
Nasiru Elrufai dai ya tsaya lallai sai a maida shi ofishin hukumar yaki da cin hanci ta ICPC inda ya ke tsare a halin yanzu.
Alamu na nuna Elrufai na fargabar shiga wajen tsaro na DSS don zai zama waje mafi tsauri na iya ganawa da jama’a ko ma kai ma sa abinci.
Iyalan Elrufai na zargin hukumar ICPC na kawo cikas wajen kai wa maigidan nasu abinci inda ICPC ta musanta hakan.
Yanzu dai za a jira a ga yiwuwar cika sharadi don nasarar belin Elrufai, kasancewar kotu ta nuna matukar ya saba ka’idar belin za ta soke izinin ko hurumin kai tsaye.
Elrufai daga jam’iyyar adawa ta ADC, ya shiga karin tsaka mai wuya a wata zantawa inda ya nuna ya na sauraron bayanan sirri na ofishin mai ba da shawara kan tsaro Malam Nuhu Ribadu.
SHUGABAN LEBANON AOUN YA CE ZAI YI ABUN AL’AJABI WAJEN DAKATAR DA YAKI DA ISRA’ILA
Shugaban Lebanon Mr.Joesph Aoun ya ce zai dau mataki mai ban mamaki ko ma marar yiwuwa a tunani don kawo karshen yaki da Isra’ila ke kawowa kan Lebanon.
Aoun ya bayyana haka ne bayan samun tattaunawar kai tsaye da Isra’ila amma hakan bai dakatar da hare-haren Isra’ila ba.
Tun samun yarjejeniyar tsagaita wuta a 17 ga watan Afrilu, Isra’ila ta cigaba da kai farmaki kan kudancin Lebaon da sunan murkushe ‘yan Hezbollah da Iran ke marawa baya.
Isra’ila har ta kan ba da wa’adi ga matsugunai a kudancin Lebanon su tashi don shirin kai farmaki.
Hezbollah ma ta ce ba ta ja da baya ba, don ta kai harin jirgi marar matuki kan wata cibiyar tsaron sojan Isra’ila a Arewacin Isra’ilar.
Zuwa yanzu daga fara wannan yaki, Isra’ila ta yi sanadiyyar kashe fiye da mutum 2,900 da jikkata wasu mutane ciki kuwa da kashe mutum 400 tun samun yarjejeniyar sulhu.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Address
Utako District
Abuja