Sahara Reporters Hausa

Sahara Reporters Hausa

Share

labarai da dumi duminsu

15/03/2026

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed na shirin komawa APC

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, Bala Mohammed, na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a cikin makon nan, idan har tattaunawar da ake yi ta yi nasara inji rahotan Arise News.

Majiyoyi sun bayyana cewa gwamnan ya gana da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da shugabannin APC, inda ya nuna sha’awarsa ta shiga jam’iyyar mai mulki.

Ana kuma tattaunawa kan sharuddan sauya shekar tasa.

Rahotanni sun ce daga cikin abubuwan da ake tattaunawa akwai ba shi tikitin takarar Sanata, amma ba za a ba shi cikakken iko da tsarin jam’iyyar APC a jihar Bauchi ba, kuma ba zai iya zabar wanda zai gaje shi a matsayin gwamna ba.

An kuma ce an bukaci gwamnan ya ba da hakuri ga Seyi Tinubu, bayan wani rikici da ya faru a bara lokacin da dansa ya soki rabon tallafin Ramadan da Seyi ya yi a Bauchi.

A bangaren Seyi Makinde da wasu jiga-jigan PDP kuwa, an bayyana takaici kan wannan shiri, suna mai cewa sauya shekar shugaban gwamnonin PDP zai iya kara raunana jam’iyyar adawa a kasar.

Sahara Reporters Hausa

Want your business to be the top-listed Media Company in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Abuja