DMA - PRESS

DMA - PRESS

Share

Born to struggle

10/02/2025

Duk Wani Brother Ko Sister Bisa Wannan Matsayar Yake, Akasin Hakan Tashi Daga Aiki Ne.

28/01/2025

JIYA MUN SHA MADADI DAGA SAYYID ZAKZAKY (H)

Wato Saboda tsananin fadi da girman da Musulunci yake dashi, da kuma irin dimbin tarin ilimin da Allahu SWT ya kimsawa wasu bayin Allah, irin Sayyid Zakzaky (H) Babu yadda za ayi ka zauna gaban su baka ji sabon abu ba, wanda baka taba ji ba, ko ka taba ji to baka jishi daidai ba sai ka tsinci kanka a gaban Sayyid Zakzaky H zaka sha mamaki yadda zai fayyace maka shi sanka sanka,

Duk tarin Malaman Nigeria ko Africa ma baki daya, baka da wani Malami da ka taba jin munasabar Yaumu Mub'as a bakin sa, har ya ware mata rana da lokaci don fayyace wa Al'ummar musu yadda aka aiko Manzon Allah SAWW da yadda ya isar da sakon da yadda Al'umma ta karbi sakon da wadanda s**a yaki sakon da wadanda s**a amsa kiran da wadanda s**a tallafawa tafiyar

Jiya fa Sayyid Zakzaky H sai da ya dauko mana tarihi tiryan tiryan tun daga kakannin Manzon Allah SAWW tsatso bayan tsatso tun daga Annabi Ibrahim da Annabi Isma'el (Alaihimus Salam) har yanzu ga Sayyid Abdulmudallib (AS) tukewa ga Sayyid Abdullahi Mahaifin Manzon Allah SAWW da Nana Aminatu (SA) da duk abubuwan tarihi da Mu'ujizozin da s**ai ta faruwa da yadda Annabawa (AS) suke magana da iyayen su mata tun suna cikin ciki, Kai ba wannan ba ma" har yadda Annabawa AS suke magana da iyayen su maza a cikin tsatson su na mazan, Ya Allah, kai Wannan Al'amari da girma yake,

Kuma Sayyid Zakzaky H ya rika kafa hujjoji da nassi daga ayoyin Alkur'ani mai girma da ingantattun hadisai, Su Malam (H) s**ace in baka sani ba ba yana nufin babu bane, ko ba haka yake ba, a a in baka sani ba kawai kace baka sani ba, kaje ka nemi sani, in kuma bakason ka sani ne, Su Malam (H) s**ace to kayi shiru da bakin ka, ka bari masu son sani su sani fakat,

Dan uwa ka nemi tashar ABS YouTube TV channel kasha madadi kaima, don dai mu kam jiya ji nayi kamar na koma sabo fil game da Imani da Manzon Allah SAWW da Ahlulbaity AS 🌹

Jagora Sayyid Zakzaky (H) Muna Rokon Allahu SWT Ya kara lafiya da nisan kwana yasa kuga bayan makiyan ku 🤲🌹

LABBAIKA YA RASULULLAH ✊
LABBAIKA YA IMAMU ALI ✊
LABBAIKA YA AL ZAKZAKY ✊

Want your business to be the top-listed Media Company in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Abuja