Fim Magazine
The best place for authentic stories about Hausa movies, culture, writing, and music
07/05/2026
Shugaba Tinubu Ya Shiga Takarar Wa’adi Na Biyu Yayin Da Mataimakinsa Shettima Ya Mika Fom ga APC
A yau Alhamis 7 ga watan Mayu ne, Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya kaddamar da neman takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a hukumance ga uwar jam’iyyar APC ta kasa.
A wani gagarumin taro da aka gudanar a dakin taro na *Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre* Mataimakin ya jagoranci mambobin jam’iyyar da s**a hada da gwamnoni, da yan majalisun tarayya, da sauran masu madafun iko na da da na yanzu, inda ya miƙa fom din neman takarar ga Shugabannin jam'iyyar a wani mataki na nuna goyon bayan masu madafun iko ga kudurin sake zaben shugaba Tinubu zango na biyu.
Da yake jawabi jim kadan bayan mika fom din, Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya bayyana shugaban a matsayin jagora mai juriya wanda ya yi nasarar Jan ragamar Najeriya zuwa tudun-mun tsira a yayinda guguwar matsalolin tattalin arziki ta so yin awon gaba da ita. Kashim ya kafa hujja da ajandar "Renewed Hope" a matsayin babban dalilin cancantar Shugaba Tinubu ga zagaye na biyu inda ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatin ta kawo sun fara samar da sak**ako mai kyau, duk da tsaurin da s**a zo da shi a karon farko.
"Kalubalen shekarun da s**a gabata ba su raunana Shugaba Tinubu ba; maimakon haka ma sai kara masa kwarewa da s**a yi," in ji Shettima, inda ya ci gaba da cewa
"Wannan gwarzantaka da kwarewa da ya kara ne ya sa mu ke fatan kara masa wata dama"
A nata bangaren, uwar jam’iyyar ta kasa ta nuna cikakken goyon bayanta ga takarar, inda
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda wanda ya karbi takardun takarar, ya ce ayyukan shugaba Tinubu a sassa daban-daban na farfado da kasar sun sa sake zaben nasa ya zama dole.
Yilwatda ya yi nuni da kyautatuwar tattalin arziki da karuwar kwarin gwiwar kasashen duniya ga makomar Najeriya a matsayin hujjojin da jam’iyyar ta dogara da su wajen amincewa da takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shi ma shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Tajudeen Abbas ya yaba da garambawul din na shugaban Tinubu, wanda ya bayyana a matsayin harsashin farfadowar kasa mai dorewa.
Ita ma kungiyar Gwamnonin APC ta bakin Shugabanta kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma wanda gwamnoni 12 s**a rufa wa baya ta nuna goyon baya na bai-daya ga takarar
Gwamnonin da s**a halarci taron su ne na jihohin Plateau, Ogun, Niger, Kaduna, Ondo, Katsina, Borno, Cross River, Taraba, Yobe, Nasarawa, da Bayelsa.
A yanzu dai mika tikitin takarar a hukumance ya kawo karshen rade-raden da ake yi game da aniyar shugaban ta neman wa'adin Mulki na biyu k**ar yadda ta bayyana irin hadin kan Shugabanni na bai daya da ake dakon gani a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC.
Shugabannin jam’iyyar sun yi kira ga mambobinsu da su fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu don "kare fatan Najeriya.".
04/05/2026
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Gwamnatin Tarayya tana so a haɗa gwiwa domin yaƙi da yaɗa labaran ƙarya
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta buƙaci a ƙara haɗin gwiwa tsakanin kafafen yaɗa labarai, hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin magance barazanar yaɗa labaran ƙarya.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja yayin bikin Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya ta shekarar 2026 da aka gudanar a Radio House.
Ya ce: “Wannan gwamnati ta ba da fifiko ga haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki a kafafen yaɗa labarai da kuma abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa domin inganta aikin jarida mai inganci da kuma yaƙi da yaɗa labaran ƙarya.”
Ya bayyana ’yancin ’yan jarida a matsayin muhimmin haƙƙi da kundin tsarin mulki ya tanada, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau da zai bai wa kafafen yaɗa labarai damar gudanar da aikin su cikin ’yanci, tsaro da gaskiya.
“Gwamnatin Tarayya ta amince da ’yancin ’yan jarida, kuma za ta ci gaba da samar da yanayin da zai bai wa kafafen yaɗa labarai damar yin aikin su cikin ’yanci, tsaro da gaskiya,” inji shi.
Ministan ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakai na ƙarfafa gaskiya da samun bayanai ta hanyar cigaba da hulɗa da kafafen yaɗa labarai, aiwatar da dokar ’Yancin Samun Bayanai, da kuma saka hannun jari a hanyoyin sadarwa na jama’a.
Ya kuma bayyana haɗin gwiwar Nijeriya da UNESCO wajen kafa Cibiyar Ilimin Kafofin Watsa Labarai da Bayanai ta Duniya (IMILI) a Abuja a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa ilimin kafafen yaɗa labarai da bayanai da kuma inganta sadarwa mai kyau a wannan zamani na dijital.
Ministan ya buƙaci ’yan jarida da su ci gaba da kiyaye ƙwarewa da ƙa’idojin aiki, yana mai jaddada cewa dole ne ’yancin aikin jarida ya tafi tare da ɗaukar nauyin da ya rataye a wuyan jama'a.
“Ainihin gwajin ’yancin ’yan jarida ba wai a cikin furucin mu yake ba, a cikin ayyukan mu yake, yadda ’yan jarida ke gudanar da aikin su cikin tsaro, yadda ake yaɗa bayanai cikin gaskiya, da kuma yadda jama’a suke amfani da su yadda ya k**ata,” inji shi.
A nata jawabin maraba, Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dakta Binyerem Ukaire, ta bayyana taron a matsayin wata dama ta ƙarfafa haɗin gwiwa da inganta wayar da kan jama’a.
Ta yi kira da a ƙara haɗin kai tsakanin hukumomi domin magance ƙalubalen yaɗa labaran ƙarya, musamman la’akari da yadda kafafen sadarwa na zamani suke ƙara yaɗuwa.
Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyar ta ta ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki domin gina tsarin bayanai mai ƙarfi da zai tallafa wa dimokiraɗiyya, haɗin kan ƙasa da cigaba mai ɗorewa.
Taron ya samu halartar Sufeto Janar na ’Yan Sanda, wanda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DCP Anthony Okon Placid, ya wakilta; da Darakta-Janar na DSS, wanda Daraktan Tsare-Tsare, M.O. Chukwuka, ya wakilta; da Babban Sakataren Hukumar Kula da Aikin Jarida ta Nijeriya, Dakta Dilli Ezughah; da kuma Shugabar Ofishin UNESCO a Abuja, wadda Shugabar Sashen Sadarwa da Bayanai, Ms Yachat Nuhu, ta wakilta.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
19 Chelsea Chibuzor Street Off NICON Junction Maitama
Abuja