Azare Media
Media
07/08/2022
Tsohon Abokin Dan Kwallon Nijeriya, Ahmed Musa Tun Na Kuruciya Na Cigiyarsa
Tsohon abokin dan kwallon Nijeriya Ahmed Musa wanda s**a taso tun yarinta a Layin Giginya dake Unguwar Bukur a garin Jos yana cigiyar aminin nasa biyo ya rasa yadda zai yi su yi ido hudu.
Mutumin ya ce Ahmed Musa ya fi saninsa da Gwamna, wato sunan da ake kiransa da shi a lokacin, sannan kuma ya bayyana cewa bacci ne kawai yake raba su da Ahmed Musa a lokacin kuruciyar su, inda a wasu lokutan ma suna kwana ne a gidajen juna, wato wani lokaci ya kwana a gidan su Ahmed Musa, shi ma kuma Ahmed Musa ya kwana a gidansu.
Saidai rahotanni sun nuna cewa Gwamna yana cikin kuncin rayuwa wanda yake bukatar tallafi.
Ya ce ya fi wata biyar yana ta kokarin ganin yadda za a yi a hada shi da Aminin nasa, amma burinsa har yanzu bai cika ba, don haka ne ya ce bari ya biyo ta kafar sadarwa ko Allah zai sa Ahmed Musan ya gani ya neme shi.
A cikin wadannan hotunan za a iya ganin Ahmed Musa da Gwamna, inda aka sa musu alama akansu.
Don haka ne ma Gwamna ya ajiye lambarsa don kira kai tsaye idan Allah ya sa Ahmed Musan ya ci karo da labarin; 07069204905
03/08/2022
Ku kiyayi Wannan Asibiti mai suna General Hospital Azare wadda akafi sani da Asibitin Ali k'wara.
Ko miyasa nace haka ??
Y'ar uwata ta dauki danta cikin yanayi na rashin lpy mai tsanani takaiga yaron wuyansa yabar ikon gangar jikinsa saboda tsananin ciwon da yake damunsa ,Bayan taje wannan Asibiti taje Emergency domin abashi agajin gaggawa , hakan ta farune bayan sallar isha'i kadan ,anbawa yaronta gado to Amma babu wani wadda yazo domin ya duba yaron har garin Allah ya waye , hakan yasa mahaifiyar yaron taje Emergency ta sake report akan abunda ke faruwa Amma babu wani wadda ya shaurareta sai wani mutum guda daga cikin ma'aikatan yazo yace mata in zata biyashi zaizo ya dorawa yaronta ruwa hakan yasa ranta ya b'aci ta fara fad'a ganin haka yasa ya janye maganar karban kud'i yazo ya dorawa yaronta ruwan wadda hakanma bayan zuwan in charge na wurin ta gane bai samo jijiyar ba kawai ya lojana kalular ne ya tafi kayansa .
Bayan sun kwana 2 a Wannan Asibiti wani daga cikin ma'aikatan yazo ya rubuta musu allurai guda 2 yace a siyo yanzu yayi masa , bayan an siyo yayi masa allurar daganan yaron ya k'ara shiga wani hali fiyeda yadda yake ada. Dasafe saiga in charge ta wannan wuri tazo taga yadda yaron yake take tambaya aka nuna mata allurar da Wannan mutumi yayiwa yaron ganin haka tasa aka kirawoshi daga zuwansa ta fara masa fad'a ashe allurar masu ciwon k'oda yayiwa yaron da baya magana kuma a lokacin take tabbatar wa mahaifiyar yaron ashe shi mai shara ne (cleaner) .
To kunji yadda Wannan Asibiti yake kuma ga yadda suke aiki bisa ganganci da kuma wasa da rayuwar mutane.
Abdullahi Ibrahim tsafi
08/07/2022
A Najeriya, ga dukkan alamu yanayin tsaro na kara tabarbarewa a kasar inda a baya bayan nan aka kai hari kan ayarin shugaban kasa da gidan gyaran hali na Kuje da ke babban birnin kasar.
Sai dai masana na ganin rashin hukunta masu sakaci na kara dagula lamarin.
Tor me kuke ganin yake janyo daburcewar al’amuran tsaro a kasar?
Wasu daga cikin batutuwan da muke fatan tattaunawa ke nan a filinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon.
© BBC Hausa
08/07/2022
Duk Wanda Yasan Ya Gudu Daga Gidan Yarin Kuje Ya Gaggauta Komawa Kafin Nan Zuwa Yamma.
-Muhammadu Buhari
07/07/2022
An k**a wasu matasa da ake zargi da satar turƙeƙen ragon Sallah
Rago
Jami’an ‘yan sandan jihar Ogun sun k**a wasumatasa biyubisa zargin satar ragon Sallar wani mutum Sadiq Abolore wanda kudinsa ya kai Naira 120,000.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Mista Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana k**a wadanda ake zargin.
Oyeyemi ya ce “An k**a wadanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da Sadik Abolore ya kai hedikwatar ƴan sanda da ke Ogijo.
Ya ce yanzu haka za a ci gaba da gudanar da bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Azare