RAMAZ Ventures

RAMAZ Ventures

Share

Ramaz Ventures is a real buainess center

25/10/2023

Ana hasashen wata zai yi 'khusufi' a daren Asabar 28 ga Oktoba, 2023 daga 9:14pm zuwa 11:26pm
Zuma Times Hausa

Photos from RAMAZ Ventures's post 25/10/2023

Zuma Times Hausa JARIDAR TARAWAITO

Gwamnan Kano ya buɗe Cibiyar Hadda da Nazarin Alƙur'ani a gidan Kwankwaso

A wani shiri daga cikin shirye-shiryen taya tsohon Gwamnan Kano Rabi'u Kwankwaso murnar cikar sa shekaru 67, Gwamna Abba Yusuf ya buɗe ya buɗe Cibiyar Hadda da Nazarin Alƙur'ani, wadda aka raɗa wa suna Majidaɗi Institute for Qur'anic Research and Advancement (MIQRA).

An sadaukar da cibiyar ne ga mahaifin Kwankwaso, Musa Sale Kwankwaso. Kuma an gina cibiyar a gidan Kwankwaso da ke kan titin Miller Road, Kano.

Sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamnan Kano, Sanusi Bature ya fitar, ya ce, "da ya ke jawabi a wurin buɗe cibiyar, Gwamna Abba ya yaba wa Sanata Rabi'u Kwankwaso dangane da wannan gagarimin tanadi da ya yi wa al'umma wajen bunƙasa ilmin addinin Musulunci."

Abba ya ce an kafa cibiyar a daidai lokacin da ya dace, idan aka yi la'akari da yawan makarantun allo da na Islamiyya da ke faɗin jihar, waɗanda ke buƙatar a narkar da su cikin tsarin makarantun zamani, domin daƙile yadda almajirai ke ta gararamba kan titina.

Gwamnan na Kano ya ƙara da cewa Sanata Kwankwaso samu gagarimar nasarar ayyukan inganta rayuwar al'umma a lokacin mulkin sa, musamman wajen bunƙasa addinin Musulunci.

Ya bada misali da aikin katange dukkan maƙabartun cikin birnin Kano, gyaran masallatan Juma'a a faɗin jiha, gina makarantun Islamiyya a ƙananan hukumomi 44.

Sai dai kuma Abba ya nuna damuwa dangane da yadda Gwamnatin da ta shuɗe a Kano, ta ƙi ƙarasa sauran makarantun da Kwankwaso bai kammala ginawa kafin cikar wa'adin mulkin sa ba.

Saboda haka sai Abba ya yi alƙawarin ƙarasa makarantun, kuma ya bada umarni ga Ma'aikatar Ilmi ta fara tsare-tsaren fara ɗaukar ɗalibai domin fara zangon karatu.

Sanata Kwankwaso ya ce an kafa MIQRA domin ta riƙa horas da mahaddata Alƙur'ani maza da mata domin samun satifiket ɗin firamare da sakandare, ta yadda za su samu hanyar zarcewa makarantun gaba da sakandare da jami'o'i.

Ɗalibai daban-daban sun jinjina wa Kwankwaso da Gwamnan Kano dangane da wannan shiri mai albarka da aka gina.

25/08/2023

SHARHIN FILM KARAN ARJUN 1997

19/06/2023

Babu wanda ke fatan ka kai shi har ma ka fi shi a rayuwa har ma yayi alfahari da hakan sai UBA
Allah ka yiwa Mahaifina

Want your business to be the top-listed Business in Azare?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Katagum
Azare