M, Galadima Rigid carpentry Limited
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from M, Galadima Rigid carpentry Limited, Artist, Bauchi yalwa lushi, Bauchi.
24/11/2023
*MAFARIN LALACEWAR KANANAN YARA.*
NA FARKO-
Shine Barin yaro akan Ra'ayin sa Na Banza / Musamman wurin yin Aski da Sanya Tufafin Banza.
Iyaye da yawa suna Sakaci da Wannan Hanyar. KUMA ita ce hanya ta farko Wajen Lalacewar Yaro.
YAKAMATA iyaye su sanya ido Sosai a wannan Bangaren .domin daga nan ne yaro yake fara zama Dan-iska.
Allah ya kiyaye.
NA BIYU SHINE=
Barin yaro Da dawainiyar Kansa. Itama wannan hanyar Tana da Matukar Mahimmanci wajen Yaki da ita / Domin daga nan ne yaro yake fara ganin cewa shima yanzu Babu mai sa shi Ko Mai hana shi. Tunda shi yake Ciyar da Kansa.
DAN HAKA ya kamata iyaye su zama Bango abin Jingina ga 'ya 'yansu.
NA UKU SHINE =
kau da kai ga Abokanan yaro. Wannan ma hanya ce mai Karfi wajen Lalacewar yaro.
IYAYE Kuna Nuna halin ko oho game da Abokanan yaran ku.
Wannan ba Karamin Kuskure bane.
Lallai ya kamata Ku sanya Idanu Sosai akan Abokanan 'ya 'yan ku.
Domin aboki yana da Matukar Tasiri Sosai Wajen Lalata Tarbiyya ko Assasa Tarbiyya.
NA HUDU SHINE=
Rashin Sanya Yaro a makarantar Islamiyya ko rashin nuna masa muhimmancin ta tun yana karami, Wanda yin hakan yake sa Yaro ya taso bai san Allah ba bai san hakkin Allah Dana AL'UMMA akan sa ba wannan yake sa Yaro ya tashi ba imani ba tausayi kan sa kawai ya sani koda kuwa zai mutu shi sai bukatar sa ta biya.
Wannan kenan A takaice.
Allah Ya Shirya Mana Zuri'armu Baki daya.
Amin Ya Hayyu Ya Qayyum
Allah yataimakemu yasa mudace da Alherinsa Ameen summa Ameen
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Bauchi Yalwa Lushi
Bauchi