Zauren Addini

Zauren Addini

Share

Kafa yanar gizo ta kungiyar masoya manzon Allah S.A.W Ahlussunna na jihar Bauchi, Nigeria.

16/05/2023

Daga shafin Dr. Aliyu Muh'd Sani

INYAS YA YI RASHIN LADABI GA ANNABI (SAW)

A cikin baitin wakarsa, Inyas ya yi amfani da kalmar "عُبيده" "Tasgiri" ga kalmar "عبده" a hakkin Annabi (saw). Inda ya ce:
وما ولد الرحمن فهو عُبيده...
Alhali "Tasgiri" kaskantarwa ne, kamar yadda Abul Baqa'i al-Ukburiy al-Bagdadiy ya ce:
"التصغير التحقير، ويقع في الكلام على ثلاثة أضرب".
اللباب في علل البناء والإعراب (2/ 158)

Ma'ana; "Tasgiri" shi ne kaskantarwa. Sai ya ambaci dalilai uku da suke sa a yi hakan, wato a wajen Malaman Nahwun Basrah.

To masu kare Inyas bisa wannan babban kuskure da ya yi suna kafa hujja da cewa: ai Inyas ya yi "Tasgirin" ne saboda girmamawa.

To, don raddi a kan haka zan rairayo mana raddin da Malam Bashiru Umar Argungun ya yi wa su Inyas din, don ya kayatar sosai.

Malam Bashir ya yi raddi wa Inyas ne ta fiskoki guda uku kamar haka:

1- "Tasgiri" saboda girmamawa "التصغير للتعظيم" abu ne da aka yi sabani a kansa, Malaman Nahwun Kufa ne kadai s**a yarda da shi. Malaman Basrah ba su yarda da shi ba. Shi ya sa al-Ukburiy bayan ya ambaci dalilai uku da suke sa a yi "Tasgiri" sai ya ce:
"وقال الكوفيون في كلامهم تحقير التعظيم كقول الشاعر من الطويل:
(وكل أناس سوف تدخل بينهم *** دويهية تصفر منها الأنامل)
وهو عندنا على التحقير، أي أن أصغر الدواهي تفسد الأحوال العظام".
اللباب في علل البناء والإعراب (2/ 158)

Saboda haka "Tasgiri" don girmamawa ba abu ne da kowa ya yarda da shi ba, saboda akwai Tufka-da-warwara a cikin hakan; ta yaya kankanta abu zai zama girmamawa?!

2- Ko da an sallama a kan za a iya yin "Tasgiri" don girmamawa, to ba za a yi "Tasgirin" duk sunan da a Shari'a wajibi ne a girmama shi ba.

Saboda haka ba za a yi "Tasgirin" "عبده" wanda aka siffanta Annabi (saw) da shi ba. Allah ya ce wa Annabi (saw):
{الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَنْزَلَ عَلَى عَبْدِهِ الْكِتَابَ وَلَمْ يَجْعَلْ لَهُ عِوَجًا (1)} [الكهف: 1]

A wani wajen ya ce:
{تَبَارَكَ الَّذِي نَزَّلَ الْفُرْقَانَ عَلَى عَبْدِهِ لِيَكُونَ لِلْعَالَمِينَ نَذِيرًا (1)} [الفرقان: 1]

A wani wajen ya ce:
{فَأَوْحَى إِلَى عَبْدِهِ مَا أَوْحَى (10)} [النجم: 10]

Cikin duka wadannan Ayoyin Allah ya kira Annabi (saw) da "عبده", wato bawansa. Don haka bai halasta a yi "Tasgirinsa" a ce: "عُبيده" kamar yadda Inyas ya yi ba.

Al-Shadibiy yana kawo wuraren da ba a yin "Tasgiri" sai ya ce:
"والثاني: أن يكون ذلك من جهة أمر خارج عن معقولية المعنى، وهو على ثلاثة أنواع:
أحدها: ما امتنع تحقيره شرعاً كأسماء الله وأسماء الأنبياء وكتب الله تعالى، وغير ذلك مما هو معظم شرعاً".
شرح ألفية ابن مالك للشاطبي = المقاصد الشافية (7/ 270)

Ka ga sai ya nuna ba a yin "Tasgirin" duk sunan da ba a wulakanta shi a Shari'a, kamar Sunayen Allah, da SUNAYEN ANNABAWA, da Sunayen Littatafan Allah, d.s.

Haka Ibnu al-Wardiy ya ce:
"التصغير
إذا لم يتوغّل الاسم في شبه حرف، كمضمر واسم فعل واستفهام وشرط، ولم يشبه صيغة تصغير كمهيمن، ومسيطر، ولم يجب تعظيمه، كأسماء الله تعالى وكتبه ورسله".
شرح ألفية ابن مالك المسمى تحرير الخصاصة في تيسير الخلاصة (2/ 702)

Haka Muhibbuddeen al-Halabiy ya fada, yana kawo sharudan "Tasgiri" sai ya ce:
"وأن يكون قابلا للتصغير بأن لا ينافيه، فلا يصغر مثل كبير وجسيم، وكذلك أسماء الله وأنبيائه وملائكته".
تمهيد القواعد بشرح تسهيل الفوائد (10/ 4859)

Kai, hatta shi Suyudiy, wanda shi ma Sufiy ne, amma da yake bayanin sunayen da ba a yi musu "Tasgiri" cewa ya yi:
"وَلَا الْأَسْمَاء الْوَاقِعَة على مُعظم شرعا كأسماء الله تَعَالَى".
همع الهوامع في شرح جمع الجوامع (3/ 391)

Kai, hatta nan kasa cikin "شذا العرف", da yake kawo sharudan "Tasgiri" cewa ya yi:
"وأن يكون قابلا للتصغير، فلا تصغر الأسماء المعظمة كأسماء الله تعالى وأنبيائه وملائكته".
شذا العرف في فن الصرف (ص: 99)

3- Sai kuma Malam Bashir ya kawo cewa; akwai wani da ya tattara wakokin Inyas, kuma Almajirinsa ne, a cikin littafinsa "آفاق الشعر", da ya ga cewa: Inyas ya saba Shari'a a wannan baiti, sai ya ci gyaransa, ya mai da baitin ya koma kamar haka:
وما ولد الرحمن بل هو عبده...
A maimakon fadin Inyas:
فهو عُبيده...
Saboda akwai kaskantar da Annabi (saw) a cikin lafazin Inyas.

Saboda haka ga shi a fili Inyas ya yi RASHIN LADABI "su'ul adabi" wa Annabi (saw), amma duk da haka sai da na ga wani da ya shahara da kare mabarnata ya kare shi - bisa jahilci da son zuciya -, ya ce: Inyas bai yi laifi ba, -wai- dan gidan Ado Musa ne kadai ya yi laifi.

Allah ya sawake, ya raba mu da jahilcin da ya ginu a kan ta'assubanci da son zuciya.

Zauren Addini

Addini A Yau - YouTube 15/05/2023

Addini A Yau - YouTube Addini A Yau

15/05/2023

Shin wannar magana s**a ce ga Annabi (saw)?

D'agã shafin Dr. Aliyu Muh'd Sani

A cikin wani faifan bidiyo an nuna hoton wani matashi dan Tijjaniyya, mai suna Nasiru Ado Musa Tafawa Balewa, daga garin Bauchi, yana karanto baitin waka daga littafin Inyas, inda Inyas din ya ce:
وما ولد الرحمن فهو عبيده...

Sai wannan matashi mabiyin Inyas ya fassara baitin da cewa:

"Allah bai haifu ba, amma Annabi a bayin ma karami ne a bayin Allah!".

Sai ya ce:
"Ma'ana shi kankanin bawon Allah ne".

To a nan wane dalili ne zai sa a siffanta Annabi (saw) da karami kuma kankani a cikin bayin Allah?

Shin wannan bai saba dalilai na Shari'a da hankali da na waki'i da suke nuna Annabi (saw) shi ne mafi girma a cikin bayin Allah ba?

Idan Annabi (saw) karami ne kankani cikin bayin Allah, to su waye manyan bayin Allahn?

Kuma miye alakar wannan baiti na Inyas da fadin Ibnu Arabiy:
مقام النبوة في برزخ *** فويق الرسول ودون الولي

Ma'ana: matsayin Annabi da Manzon Allah duka suna kasan matsayin Waliyyi ne. Don haka Waliyyai irin su Tijjani, Inyas suna sama da Annabawa da Manzanni, don haka - bisa wannar magana - Waliyyai za su zama su ne manyan bayin Allah, Sai Annabawa, sai kuma Manzanni su ne kananan bayin Allah.

Subhanallah!
Wannan tunani bata ne mai girma, wanda ya saba wa Addinin Muslunci.

Tambaya ta gaba: zuwa yanzu wani kokari Hukumar Shari'ar Muslunci ta Jihar Bauchi ta yi?

Ina irin su Prof. Maqari, Abubakar Madatai d.s, wane mataki s**a dauka a kan wannan magana, don kare matsayin Annabi (saw)?

Muna fatan za ku tashi tsaye don yin abin da ya dace, a kan wannar magana mai muni, mai warware Nassoshin Addinin Muslunci.

©Addini A Yau

Zauren Addini Kafa yanar gizo ta kungiyar masoya manzon Allah S.A.W Ahlussunna na jihar Bauchi, Nigeria.

15/05/2023
Want your place of worship to be the top-listed Place Of Worship in Bauchi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Jahun
Bauchi