Bauchi Daily Post

Bauchi Daily Post

Share

Jarida ce da za ta riƙa kawo muku labaran jihar Bauchi da kewaye daga 5STARS MEDIA PRODUCTION.

Photos from Bauchi Daily Post's post 25/12/2025

RABON KAYAN KIRSIMETI :
Uwargidan Gwamnan jahar Bauchi Dr. Aisha Bala Mohammed ta Sanya farinciki wa al'umman kiristoci a jihar Bauchi a yayin bikin kirsimeti.

Uwargidan gwanmnan Tayi rabon kayan abinci wa yan uwa ma abota addinin kirista don ganin cewa kiristoci a jihar sunyi bikin na bana cikin farin cikin.

19/10/2025

DA DUMI-DUMI: Shahararren Mawakin Gargajiya Na Bauchi, John Zuya, Ya Mûtû

An bayyana mutuwar fitaccen mawakin gargajiya kuma mai barkwanci daga garin Tafawa Balewa, jihar Bauchi, John Zuya, wanda aka fi sani da John Mai Molo, bayan da ake zargin an sa masa guba.

Rahotanni sun nuna cewa John Zuya, wanda kwanan nan ya dawo daga jihar Lagos inda ya je yin sana’arsa ta waka, ya rasu da safiyar jiya bayan da wasu da ake zargin abokansa ne s**a kai shi gidan cin abinci, s**a sanya masa guba mai karfi ba tare da ya sani ba.

Shaidu sun bayyana cewa mamacin ya fara nuna alamun ciwo mai tsanani kafin daga bisani ya riga mu gidan gaskiya. An kai gawarsa zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi, domin gudanar da bincike don gano musabbabin mutuwarsa da kuma wadanda ke da hannu a lamarin.

Marigayi John Zuya ya kasance mutum ne mai fara’a, barkwanci da baiwa ta musamman a fagen waka. Ya shahara a yankin Bauchi da sauran sassan ƙasa saboda irin wakokinsa na gargajiya da nishadantarwa.

Photos from Bauchi Daily Post's post 16/10/2024

Gwamnan jihar Jigawa ya jagoranci jana'izar mutane sama da 100 da s**a kone sanadiyar tankan Fetur jiya da dare a garin Majia jihar Jigawa.

Inda aka tona babban kabari aka saka duka gawarwacin ciki. Muna Addu'ar Allah ya jikansu ya yafe musu kura kuransu, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani.

Want your business to be the top-listed Media Company in Bauchi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


Ahmadu Bello Way
Bauchi
740102