Ibrahim Salihu

Ibrahim Salihu

Share

PATIENCE

21/02/2025

Sanarwa daga CUPS!
Jama'a barkanmu da warhaka. Ina murnan sanardaku cewa mun sami mutane dubu goma sha biya da dari bakwai da hamsin (15,750) wadanda s**a yi ragista domin samun training na Computer and ICT na CUPS. Alhamdulillah.

Duk wadanda s**a yi ragista suyi kokari su shiga dandalinmu na Telegram, domin a wajen ne zamuyi training din. Ku dubi sashin comments domin samun link din.

Insha Allah zamu rufe registration form yau da karfe goma na dare agogon Najeriya. Zamuyi training wadannan rukunin farkon. Idan mun kammala sai kuma mu sake diban wasu. Zamu ci gaba da yin hakan sai har mun kammala mutane dubu dari. Idan Allah Ya sa kome ya tafi daidai, toh zamu maimaita wannan tsarin sai har munyi training mutane million daya.

Daga daren yau ne muke son fara gwajin training din. Idan kome ya tafi daidai Insha Allah zamu fara training wurjanjan ranan Lahdi 2/3/2025. Allah Ubangiji Ka bamu gagarumar nasara akan wannan tafiya. Amin Ya Rabbi.

Jama'a na barku lafiya

Dr Idris Ahmed.
CUPS.
21/2/2025.

21/02/2025

Jama'a barkanmu da warhaka. Alhamdulillah, mun sami mutane wajen dubu goma sha biyar da dari biyar (15,000) sunyi ragista domin samun horaswa na Computer and ICT wadda CUPS ta dau nauyi. Toh amma mutane 10,000 kadai s**a shiga dandalinmu na Telegram. Wannan ya nuna cewa mutane 5,500 ba zasu sami daman yin training ba, domin a dandalinmu na Telegram ne zamuyi training din. Saboda haka duk wadda bai shiga dandalinmu na Telegram ba, toh ya garzaya ya shiga. Ga link din a sashen comments. Na barku lafiya.

16/02/2025

Sanarwa Daga CUPS!
Jama'a barkanmu da warhaka. Ina murnan sanardaku cewa registration form na karatun Computer and ICT na CUPS ya fito. Kowa da kowa zai iya cikewa. Mazauna kudu da kasashen waje suma suna iya cikewa. Kuna iya cike form din da salula ko da computer.

Registration kyauta ne. Horaswa na sati goma sha biyar (15) shima kyauta ne. Laboratory hands-on experience shima kyauta ne. Daga karshe, duk wadda yayi kokarin kammala training har na tsawon sati 15, zai sami Certificate daga kassaitaccen Jami'a. Wannan Certificate din shima kyauta ne.

Muna da kudurin training matasanmu da zawaranmu da marayummu su dubu dari (100,000) a zagaye na farko. Toh amma daga bisani muna fatan zamuyi training mutane million daya (1,000,000).

Jama'a ku duba a sashen comments akwai link na registration form din. Zamu saka link din kuma a dandalinmu na Telegram.

Jama'a don Allah kada kuyi watsi da wannan daman. Kudin horaswa da laboratory hands-on experience da certificate ya kai kamar naira dubu dari (N100,000).

Jama'a na barku lafiya.

Dr. Idris Ahmed.
CUPS.
16/2/2025.

31/01/2025

رَبَّنَا ٱغۡفِرۡ لِي وَلِوَٰلِدَيَّ وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ يَوۡمَ يَقُومُ ٱلۡحِسَابُ

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Biu?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Biu