Real Musa Ibrahim
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Real Musa Ibrahim, Actor, Dutse yalwawa, Dutse.
15/04/2025
Trump ya kira Shugaban China Xi Jinping a "mutum mai basira"
duk da yaƙin kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu
Mintuna 56 da s**a wuce
Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙara haraji kan ƙasashe
masu yawan gaske na duniya, ciki har da daɗaɗɗun abokan
hulɗar Amurka.
Sai dai awanni kaɗan bayan ƙarajin harajin ya fara aiki, ranar 9
ga watan Afrilu, Trump ya sanar da dakatar da ƙarin harajin na
tsawon kwana 90 kan kaya da dama, inda ya mayar da hankali
kan taƙaddama da ƙasa ɗaya - China.
Sanarwar ta sanya wasu masharhanta na tunanin ko dama tun
farko China yake hara domin rage mata tasiri a fagen kasuwanci
na duniya baki ɗaya.
Tun da farko Trump ya saka wa kayan da ake kai wa ƙasarsa
daga ƙasashen duniya haraje-haraje, ciki har da ƙawayen
Amurka.
Amma 'yan awanni bayan fara aiki da sabon harajin a ranar 9
ga watan Afrilu, sai ya sanar da dakatar da shi na tsawon kwana
90, inda ya mayar da hankali kan yaƙin kasuwanci da China.
Sanarwar ta sa wasu ƙwararru ke tunanin da ma Trump ya daɗe
yana haƙon China.
Tun bayan rantsar da shi a watan Janairu, Shugaba Trump ya
mayar da hankali kan kasuwanci inda ya bijiro da sababbin
haraji iri-iri, yana mai iƙirarin cewa abokan hulɗa na zalintar
Amurka.
Umarnin shugaban ƙasa da ya sanya wa hannu ranar 2 ga
watan Afrilu, shi ne mafi jawo cecekuce wanda a ciki ya sanya
wa ƙasashen duniya da yawa harajin da ya jawo karyewar
kasuwannin hannun jari a duniya, abin da kuma ya haddasa
fargabar faɗawa yaƙin kasuwanci.
Bayan sanar da tsagaitawa ta kwana 90 kan ƙasashe, fadar
White House ta ce da ma shirin Trump ne ya saka haraji mai
yawa kafin ya sassauta domin tattaunawa da ƙasashe ɗaya
bayan ɗaya.
Amma kuma babu China ckin waɗanda aka sassautawa.
A madadin haka, Trump ya saka wa China harajin kashi 145
cikin 100. Jami'an China sun ce da ma manufar ita ce hukunta
China da kuma tilasta mata hawa teburin tattaunawa.
"Su ne babbar matsalar Amurka a fagen kasuwanci," a cewar
Sakataren Kasuwanci na Amurka Scott Bessent, "kuma su ne
ma matsalar duniya baki d
09/04/2025
Masha Allah
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Website
Address
Dutse Yalwawa
Dutse