Jewel Multimedia
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Jewel Multimedia, Media/News Company, Gombe.
02/11/2025
Ina Matafiya Wannan Hanyar A Wace Jiha Take A Nigeriya?
24/10/2025
HISBAH Pantami Yamma Ta Shayar Da Bayin Allah Ruwan Sanyi A Gombe
A yau Juma’a, rundunar Hisbah Pantami Yamma ta gudanar da wani aikin alkhairi mai matuƙar jan hankali na shayar da bayin Allah ruwan sanyi (pure water) a masallatai biyu a cikin birnin Gombe.
Aikin, wanda aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Malam Ibrahim M. Labaran, ya gudana ne a Masallacin Juma’a na Maizare (Ahajas) da kuma Masallacin Juma’a na Madina Quarters, Opposite Wuri Biriji, inda aka raba kwalaben ruwa ga masu halartar sallar Juma’a.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutum 660 ne s**a amfana da wannan shirin, wanda aka yi da nufin rage ƙishirwa da taimaka wa al’umma a wannan lokacin na zafi mai tsanani.
Da yake jawabi ga wakilanmu, Malam Ibrahim M. Labaran ya bayyana cewa wannan aiki wani ɓangare ne na shirye-shiryen Da’awah and Relief Organization Gombe wajen ganin an karfafa taimakon juna da ciyar da al’umma gaba.
Wannan ba kawai rabon ruwa ba ne, alkhairi ne da nufin ƙara haɗin kai da nuna kulawa ga bayin Allah. Muna fatan sauran ‘yan uwa musulmi za su yi koyi da irin wannan aiki, in ji shi.
A wasu wurare da aka kai ruwan, jama’a sun bayyana farin cikinsu da godiya ga rundunar Hisbah, inda s**a ce a wannan lokaci na zafi, ruwan sanyi ya zama wata ni’ima ta musamman.
Aikin ya kuma jawo yabo daga masu ibada da mazauna yankunan Maizare da Madina Quarters, inda aka yaba da yadda rundunar ke ci gaba da shirya ayyuka masu amfani ga al’umma.
Hakika, wannan shayarwa ta zama wata gagarumar nasara ga rundunar Hisbah Pantami Yamma, kuma ta zama abin koyi ga sauran kungiyoyi masu kishin al’umma a jihar Gombe.
#
19/10/2025
LABARI MAI DADI
YANZU-YANZU: Kamfanin ABBA PANTAMI DATA LTD, ya rage muku farashin Data, kowa ya duba Application dinshi domin more garabasa.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Website
Address
Gombe
1238