Jibwis Hashidu

Jibwis Hashidu

Share

𝐂𝐚𝐥𝐥 𝐭𝐨 𝐢𝐬𝐥𝐚𝐦

Photos from Jibwis Hashidu's post 29/03/2026

MAKARANTAR UBAYYU BIN KA'AB LITTAHFIZUL QUR'AN HASHIDU TA GABATAR DA WALIMAR SAUƘAR KARATUN ALKUR'ANI MAI GIRMA TARE DA RUFE MUSABAƘAR ALKUR'ANI MAI GIRMA KARO NA BIYU(2).

Yau cikin ikon Allah aka gudanar da waliman sauƙan karatun Alkur'ani mai girma na ɗaliban makarantar Ubayyu bin Ka'ab littahfizul Qur'an Hashidu Wanda take ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar malamai na ƙungiyar Jama'atul Izalatil Bidi'ah wa iƙamatissunnah na garin Hashidu Malam Abdullahi Kawule.

Taron wanda ya kasance abin farin ciki ga malamai,iyayen yara da sauran al'umman gari kuma duba da yanda ya ƙayatar, kuma wannan shine karo na biyu bayan ɓude wannan makarantar kuma a yau anyi walimar ɗaliban maza da mata guda ashirin da hudu(24) a babban ɗakin taro na makarantar sakandare ta hashidu.

A nasa jawabin jagoran wannan makarantar Malam Abdullahi Kawule "ya nuna farin cikinsa bisa yadda al'umma s**a amsa gayyatar tare da bada hadin kai, kuma ya bayyana cigaba da nasarori da wannan makarantar ta samu tun bayan kafata shekara uku da s**a wuce zuwa yanzu".

Sheikh Nasir Umar Albanin Izala wanda ya kasance babban baƙo a wajen Wannan taron ya gabatar da takaitaccen nasiha da jan hankali ga ɗalibai "game da ƙara dagewa a kan karatun su kuma ya ƙara jan hankalin iyayen yara da su kasance masu bibiyan halin da yaransu suke ciki domin basu tarbiyya wacce ta dace".

Mai girma Hakimin Hashidu wanda ya samu wakilcin Dan isan Hashidu ya yaba da irin ƙoƙari da tasiri da wannan makarantar take wajen gyaran tarbiyyar yara da basu ilimi mai inganci acikin wannan gari mai albarka.

Daliban sun nuna hazaƙa da himma inda s**a rera karatun Alkur'ani mai ratsa zuciya daga bisani kuma s**a gudanar da wasan kwaikwayo na larabci akan "Ilimi" sa'annan aka gudanar da abinda ya shafi "ulumul Ƙur'an".

Daga karshe an bada kyaututtukan ga waɗanda s**a zamo zakaru a gasar karatun Alkur'ani da aka gudanar na Wannan makaranta tun daga mataki na ɗaya har na uku a kowane fanni(Category). Wanda Sani Muhammad shi ya zama gwarzon shekara a matakin Izu talatin (30) Sai Habiba Muhammad gwarzuwa a bangaren Mata a matakin Izu ashirin (20).

Taron ya samu halartar shugaban ƙungiyar Jama'atul Izalatil Bidi'ah wa iƙamatissunnah; Malam Ibrahim Babayo, Shugaban kwamitin Marayu;Malam Sani Haladu, Chief Imam na Masallacin jibwis hashidu Imam Muhammad bin Umar,Dr. Bala Mohammed Hashidu, sauran shugabannin gari da iyayen yara.

✍️✍️✍️
Mahmud Abubakar Hashidu

Photos from Jibwis Hashidu's post 27/03/2026

Sharan Fage na wa'azin jaha da za'a gudanar a garin Gombe-Abba, karamar hukumar Dukku a gobe asabar , bisa umurnin Shugaban ƙungiya na jaha Eng.Salisu Muhammad Gombe ,Sheikh Nasir Umar Albanin Izala ya ziyarci garin domin gudanar da karatuttuka gabannin gudanar da gagarumin wa'azi na jaha da za'a gudanar a gobe da yardar Allah

Allah ya bada nasara🤲

Photos from Jibwis Hashidu's post 20/03/2026

HOTUNA: Atisayen motsa jiki na ƴan agajin Jama'atul Izalatil Bidi'ah wa iƙamatissunnah na garin Hashidu bayan kammala sallar Eid.

Allah ya maimaita mana 🤲🏾

Photos from Jibwis Hashidu's post 20/03/2026

HOTUNA:Yanda aka gudanar da sallar Eid al-fitr a masallacin izala na garin hashidu.
تقبل الله منا ومنكم صالح الأعمال

Want your place of worship to be the top-listed Place Of Worship in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Gombe
343321