Zakarim INFO.

Zakarim INFO.

Share

Aslm Alaikum Yan uwa ina mai marabtanku da ziyarar wannan page din mai Albarka, maraba sosai � ~Da

03/09/2025

Hi

03/09/2025

Matsalar tsaro: Dole ma mu kirkiri ƴansandan jihohi - Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce kafa rundunar ’yan sandan jihohi ya zama dole, domin magance matsalar tsaro da ke damun ƙasar.

Tinubu ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da ya karɓi tawagar manyan ’yan asalin Katsina ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Radda.

Ya umarci hukumomin tsaro da su sake duba dabarun aikin su a Katsina, tare da tabbatar da rahoton yau da kullum, sannan ya sanar da amincewar gwamnati kan ƙarin sayen jiragen leƙen asiri (drones).

Shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa za a tura kayan aikin soja na zamani da na’urorin sa ido a jihar, tare da duba yiwuwar ƙarfafa mafarauta da aka tura.

Tinubu ya jaddada cewa matsalar tsaro ba za ta gagari gwamnati ba, yana mai cewa: “Za mu kafa ’yan sandan jihohi, za mu magance rashin tsaro, dole mu kare ’ya’yanmu, mutanenmu, da wuraren ibadarmu.”

Ya kuma tabbatar da ci gaba da kiyaye amanar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yana mai cewa Buhari ya bar wa Najeriya tarihin nasara.

A nasa jawabin, gwamna Radda ya gode wa shugaban ƙasa kan goyon bayansa ga jihar, yayin da tsohon gwamna Aminu Masari da Wazirin Katsina, Ibrahim Ida, s**a yaba da ayyukan ci gaba da Tinubu ke aiwatarwa a jihar, tare da neman ƙarin kulawa musamman a fannin tsaro da filin jirgin sama na Katsina.

Want your business to be the top-listed Media Company in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Cheheniya Police Barrack Gombe
Gombe
760001