Bitkova Digital Hub
Waye Mu?
20/03/2026
Sunnonin Sallar Eidul Fitr da Yakamata mu sani.
Yakai ɗan uwa mai albarka kayi ƙoƙarin domin dacewa da sunnar fiyayyen halitta Annabi Muhammad ﷺ gobe ranar Eidin Sallar Azumi ka lizimci waɗannan abubuwan domin samun ladar koyi da Annabi Muhammad ﷺ, gasu kamar hakan:
1⃣Wanka Domin Sallar Eid
(الموطأ للإمام مالک 432)
2⃣ Sanya turare, Sanya Tufafi masu kyau.
(المطالب العالیة 1:85)
3⃣Cin Abinci kafin Zuwa Sallar Eidi (Eidil Fitr)
( صحیح البخاری 953)
4⃣Tafiya Kasa Zuwa Eidi
(530 سنن الترمذی)
5⃣ Sauraron Khudubah bayan gama Sallar Eidi
( صحیح سنن ابن ماجه1073 )
6⃣Chanza Hanya yayin dawowa daga Sallar Eidi
(صحیح البخاری 986)
7⃣ Addu'o'in yayin Haduwa da mutane
" تقبل الله منا و منکم"
(مسند الإمام أحمد)
8⃣ Nuna farin ciki da Nishadi
(صحیح مسلم)
Domin samun lada daga Allah kuyi sharing ɗinsa domin ƴan uwa su amfana. Allah ya karɓa mana.
Rubutawa da gabatarwa
©️ Engr Aliyu Almustapha
14/03/2026
Ramadan Reminder| Day 25
Manzon Allah ﷺ ya ce:
Azumi da Al-Qur’ani za su yi ceto ga bawa a Ranar Alƙiyama.
Azumi zai ce:
“Ya Ubangiji! Na hana shi abinci da sha’awa da rana, ka ba ni izinin in yi masa ceto.”
Al-Qur’ani kuma zai ce:
“Ya Ubangiji! Na hana shi barci da dare saboda yana karantani, ka ba ni izinin in yi masa ceto.”
Sai Allah Ya ba su izinin su yi masa ceton.
(Sahih Jam'i 3882)
Ma’ana a takaice:
Wannan hadisin yana nuna cewa azumi da karatun Al-Qur’ani ibadu ne masu girman lada, har ma za su tsaya su kare mutum a Ranar Alƙiyama.
Darussa daga hadisin:
Azumi ibada ce da za ta yi ceto ga mutum a lahira.
Karatun Al-Qur’ani musamman a Ramadan yana da babbar lada.
Hada azumi da karatun Al-Qur’ani yana daga cikin manyan ayyukan Ramadan.
Allah ya sa azuminmu da karatun Al-Qur’aninmu su zama dalilin cetonmu a Ranar Alƙiyama.
Kada ku manta muna cigaba da registration na Ajin Cryptocurrency 2026A
🌍https://bitkova.com/our-hub
11/03/2026
Ramadan Reminder| Day 22
Daga Abdullah ibn Umar (Allah Ya yarda da su duka) ya ce:
“Manzon Allah ﷺ yana yin ’itakafi a cikin kwanaki goman ƙarshe na Ramadan.”
Ma’anar hadisin a taƙaice:
Ikaaf shine zama a masallaci don tsarkake lokaci daga duk abin duniya, yin ibada, addu’a, karatun Alƙur’ani, da tunani game da Allah.
Darussa 3 daga wannan hadisi:
1. Muhimmancin kwanaki goma na ƙarshe: Wannan hadisi yana nuna cewa Manzon Allah ﷺ yana mai da hankali sosai a cikin kwanaki goma na ƙarshe, domin samun lada da kusantar Allah.
2. Tsarkake lokaci don Allah: Yin ikaaf yana koya mana yadda mu ware lokaci na musamman don ibada, nesa da duniya da damuwarta.
3. Ilimi da ibada tare: Ta hanyar kasancewa cikin ikaaf, mutum yana ƙara karatun Alƙur’ani, addu’a, da tsarkake zuciya, wanda yake ƙarfafa dangantaka da Allah.
Allah Ya sa mu dace da wannan lada a cikin kwanaki goma na ƙarshe.
Kada ku manta muna cigaba da registration na Ajin Cryptocurrency 2026A
🌎https://bitkova.com/our-hub
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the school
Telephone
Website
Address
Gombe