Madubi - H

Madubi - H

Share

The Only Hausa News Blog You Can Trust

09/07/2026

Sheikh Sani Isah Kano Ya Sanar da Ficewarsa Daga Tafiyar Pantami.

Daga: Haji Shehu

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Isah Kano, ya sanar da cewa ya janye daga "tafiyar Pantami", bayan wata takaddama da ta ɓarke tsakaninsa da wasu daga cikin magoya bayan Sheikh Isa Ali Pantami a shafukan sada zumunta.

Malamin ya bayyana hakan ne cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa, inda ya ce ya ɗauki matakin ne bayan cece-kuce da s**a biyo bayan goyon bayan da ya nuna wa Sheikh Auwal Albani Gombe.

A cikin bidiyon, Sheikh Sani ya ce ba zai ci gaba da kasancewa cikin tafiyar ba, yana mai cewa:

"Na fita daga tafiyar Pantami. Idan daga cikinku akwai wanda ya isa ya cire ni daga Musulunci, to ya yi."

Ya kuma bayyana cewa tun da farko manufarsa ita ce kare martabar malamai da abin da ya gaskata, ba wai kare wani mutum ɗaya ba.

Lamarin dai ya jawo muhawara a kafafen sada zumunta, inda mabiyan bangarorin biyu ke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan matakin da malamin ya ɗauka.

09/07/2026

Ku Bude Wuta Kan Ƴan Bindiga Da Zarar Kun Gamu Da Su, Kar Ku Jira Umurnin Kowa - Umurnin Ministan Tsaro Ga Sojoji.

Ministan Tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya umarci jami'an rundunar soji da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta harbe tare da hallaka 'yan bindiga da 'yan ta'adda da zarar sun ci karo da su, ba tare da jiran wani ƙarin umarni daga kowa ba.

Musa ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a birnin Sakkwato, yayin ƙaddamar da motocin sulke guda 62 da babura guda 320 da gwamnatin jihar Sakkwato ta saya domin amfanin jami'an tsaro da ke aiki a faɗin jihar.

An ruwaito cewa kayayyakin tsaron da aka ƙaddamar sun kai kimanin darajar naira biliyan 27.7.

Da yake jawabi a wajen taron, Ministan ya ce ya zama dole jami'an tsaro su ɗauki matakin da ya dace idan s**a gamu da 'yan bindiga ko 'yan ta'adda, maimakon su tsaya jiran umarni.

"Ina sake jaddada wannan ga dukkan jami'an rundunar soji da sauran hukumomin tsaro. Da zarar an tura ku aiki, kada ku jira umarnin kowa kafin ku harbe ko ku hallaka ɗan bindiga ko ɗan ta'adda," in ji Musa.

Ya ƙara da cewa duk jami'in da ya ƙi ɗaukar mataki saboda yana jiran umarni, za a ɗauke shi tamkar mai taimaka wa 'yan bindiga.

"Duk wanda ya ƙi harbe ko hallaka ɗan bindiga ko ɗan ta'adda da sunan yana jiran umarni, za mu ɗauke shi kamar ɗan bindiga ne." - Inji Ministan.

Ministan ya kuma tunatar da jami'an tsaro cewa kuɗaɗen da aka yi amfani da su wajen sayen waɗannan kayan aiki na gwamnati ne da kuma harajin 'yan Najeriya, saboda haka wajibi ne a kula da su yadda ya kamata.

Ya gargadi jami'an da kada su yi sakaci ko su lalata kayan aikin, yana mai cewa bayan shekara guda za a sake duba yadda aka yi amfani da su da kuma irin kulawar da aka ba su.

09/07/2026

Munyi Nasarar Kara Albashin Sojoji Daga Naira 49,000 Zuwa Naira 100,000.

Ministan Tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ƙara mafi ƙarancin albashin sojojin ƙasar daga Naira 49,000 zuwa Naira 100,000 a wata, domin inganta walwala da jin daɗinsu.

Naija News ta ruwaito cewar, Musa ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan ƙoƙarin gwamnati na bunƙasa jin daɗin jami'an tsaro, inda ya ce duk da wannan ƙarin albashi, har yanzu rundunar sojin Najeriya na fama da ƙarancin kuɗaɗen gudanar da ayyukanta.

A cewarsa, Janar Christopher, a baya soja na karɓar albashin Naira 49,000 ne kacal a wata, amma yanzu mafi ƙarancin albashinsa ya kai Naira 100,000.

Da aka tambaye shi ko kasafin kuɗin da ake warewa ma'aikatar tsaro ya wadatar, Janar Musa ya amsa da cewa: "Bai isa ba."

Har ila yau, ya musanta zarge-zargen da ke yawo cewa ana ba sojoji abinci mara inganci, yana mai cewa waɗannan ikirari ba su da tushe.

08/07/2026

Rarara Da Ƴan Kannywood Ne Kaɗai Ke Tallata Tinubu A Arewa - Inji Dr. Babayo Sule.

Dr. Babayo Sule, malamin jami'a kuma mai sharhi kan harkokin siyasa daga Jihar Gombe, ya ce yadda mawaki Dauda Kahutu Rarara da wasu fitattun 'yan Kannywood ke ci gaba da tallata Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Arewacin Najeriya ya nuna cewa manyan 'yan siyasa sun ja da baya wajen kare shugaban.

Dr. Sule yace "Ai abin matuƙar farin ciki ne. Wannan yana nuna cewa su kaɗai s**a rage masa a Arewa, tunda har gwamnoni da manyan 'yan siyasa na tsoron tallata shi, sai 'yan bariki."

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan rawar da Rarara da wasu 'yan Kannywood ke takawa wajen yaɗa manufofi da tallata Shugaba Tinubu a Arewacin Najeriya.

Want your business to be the top-listed Media Company in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Gombe