AMT News

AMT News

Share

A media and technology company providing news coverage, documentary production, content creation, digital communication, advertising, and ICT services.

Photos from AMT News's post 01/06/2026

Ina Gombawa kuzo mu gwada waye yafi dacewa da gwamnan Gombe, Pantami ko Jamilu?

akafta

28/05/2026

Kwankwaso ya goyi bayan takaran Tijjani Gandu dari-bisa-dari

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana dalilin da ya sa ya tsayar da fitaccen mawaƙin tafiyar Kwankwasiyya, Tijjani Hussaini Gandu, takarar ɗan majalisar jihar Kano a jam’iyyar NDC.

Kwankwaso ya ce Tijjani Gandchannelstv.comu ya shafe shekaru yana yi wa tafiyar Kwankwasiyya hidima ta hanyar amfani da basirarsa da tunaninsa wajen yaɗa manufofin tafiyar.

Ya bayyana cewa hakan ne ya sa aka ga ya dace a ba shi damar tsayawa takara domin wakiltar al’umma.

Jam’iyyar NDC ta tsayar da Tijjani Gandu takarar kujerar majalisar jihar Kano ne a mazabar Gwale.

Ayatullahi Tage

28/05/2026

Alhajin Gombe Ya Rasu A Saudiyya Yayin Aikin Hajjin 2026

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Gombe ta sanar da rasuwar ɗaya daga cikin alhazan jihar da ke gudanar da aikin Hajjin bana a ƙasar Saudiyya.

Mamacin mai suna Alhaji Babawuro Abdulkadir, ɗan ƙaramar hukumar Gombe, ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya.

A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na hukumar, Mohammed Mohammed, ya fitar, an ce mamacin ya rasu ne a Muzdalifah jim kaɗan bayan sallar Isha’i, bayan dawowarsa daga filin Arafat inda alhazai ke gudanar da ɗaya daga cikin manyan rukunan Hajji.

Hukumar ta yi addu’ar Allah ya gafarta masa, ya jikansa da rahama, sannan ya bai wa iyalansa da ’yan uwansa haƙurin jure rashinsa.

Rasuwar na zuwa ne yayin da dubban alhazai daga sassa daban-daban na duniya ke ci gaba da gudanar da sauran ibadun Hajjin shekarar 2026 a ƙasar Saudiyya.

Want your business to be the top-listed Media Company in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Gombe