Mus'abmk

Mus'abmk

Share

Change de Chang 2023

Photos 09/02/2017

Ya Allah, Ya Rahman,Ya Aziz, Ya Kayum Ya Zuljalali Wal Ikram Ya Allah Kabawa Wanann Bawa Naka Lafiya Tareda Nisan Kwana Karabashi Daga Sharin Makiya Da Duk Wani Sihiri Da Wasu Suke Yi Don Suga Bayan Wanann Bawa Naka Ya Allah Karka Basu Iko Ya Allah Kasa Yafi Karfin Su Ako Inna Alla Ka Kara Kare Mana Baba Buhari

Photos 02/01/2017

Babu Wani Mara Gaskiyar da Zan 'Dagawa 'Kafa Cewar Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta sassautawa duk wanda aka k**a da cin hanci da rashawa ba domin tana nan daram kan 'kudurinta na kawar da almundahana a Najeriya.

Buhari wanda ya ke jawabi a sa'kon taya murnar sabuwar shekara ga 'yan Najeriya ya ce za a binciki duk wad'anda ake zargi da rashin gaskiya da karkatar da abinci da kud'ade'n da aka ware don taimaka wa 'yan gudun hijira da inganta sansanoninsu.

Buhari wanda ya ce makomar 'kasarnan ta dogara kan gwargwadon nasarar da ta samu wajen ya'kar rashawa, ya kuma jaddada aniyarsu ta bin doka da oda wajen yin wannan ya'ki.

Kwanakin baya ne dai sanatoci s**a zargi Sakataren Gwamnatin Buharin da sab'a doka wajen bai wa kamfaninsa kwangila da kuma amfani da ofishinsa wajen ware ma'kudan miliyoyin nairori don sare ciyayi a sansanonin gudun hijira.

Photos 28/12/2016

Mun sami Nasarori a har kar Noma, an bankado sunayen boge sama da 50,000 sannan gwamnati za ta dauki nauyin katatun 'yan matan Chibok har zuwa Jami'a - BUHARI
-------------------------------

Babban mai taimaka wa shugaban kasa MUHAMMADU BUHARI akan harkar watsa labarai Garba Shehu yace a wannan shekaran gwamnati ta rage asaran da take yi na biyan albashi a kowani wata ga ma'aikatan boge.

Garba Shehu yayi bayanin hakanne a wata ganawa da yayi da 'yan jarida a Abuja.

Yace gwamnati na biyan kudin da ya kai biliyan 200 a kowani wata amma bayan ta gama binciken sahihan ma'aikatan gwamnatin tarayyan sai ta gano cewa sama da ma'aikata 50,000 na boge ne wanda wadansu ne ke amfani da sunayensu domin wawushe kudaden gwamnati sannan gwamnati ta k**a wadansu manyan ma'aikatan ta guda 11 da suke da hannu akan hakan kuma ta mika su ga hukumar EFCC domin a bincikesu.

Garba Shehu ya kara da cewa gwamnatin Buhari ta zake da sai ta kawar da duk wani irin cin hanci da rashawa a kasar domin kuwa zata cigaba da tantance ma'aikatan ta domin tabbatar da ta gano masu shirya irin wannan aiki da karerayi.

Da yake magana akan ‘yan matan Chibok wanda aka ceto su daga hannun Boko Haram Ya ce gwamnati ta dauki nauyin kula da ‘yan matan amma a yanzu haka mutane da kungiyoyi dayawa da ke kasar nan da wadansu daga kasashen waje sun nuna suna son su dauki nauyin ‘yan matan musammman akan abinda ya shafi karatunsu k**ar wani hanshakin mai kudi mai suna Robert Smith kuma mazaunin kasar Amurka da ya dauki alkawarin biyan kudin makarantar ‘yan matan guda 21 da kuma sauran da sojoji za su ceto har zuwa jami’a, da kuma gidauniyar Murtala Muhammed da ta yi irin wannan tayin.

Duk da haka wasu iyayen ‘yan matan sun koka da yadda ‘yan sandan farar hula ba su bar ‘yan matan sun je gidajen iyayen su ba domin su yi bukin krismati duk da cewa suna cikin garin Chibok.

Shugaban ‘yan sandan farar hulan wato SSS yace dalilin yin haka shine domin sun sami ‘yan matsaloli ne kan tsaron yan matan.

NOMA

Garba Shehu yayi bayanin cewa ganin yadda shugaban kasa ya ke da muradin ganin cewa aikin gona ya dawo da martabarsa a kasa Najeriya a wannan shekaran gwamnati ta taimakawa manoma sannan a na sa ran za'a samu kayan gona wadatacce domin ci da siyarwa a kasa Najeriya da kasashen waje kuma hakan ya farantawa manoma rai domin a yanzu haka sababbin tsaruka da shirye shirye ne gwamnati ta fara domin samun ire-iren wadannan nasarori a damiman badi.

Wani abin da ya farantawa manoma ciki shine yadda gwamnati ta hana shigowa da kayan abinci musamman shinkafa kuma ta shawarci manyan kamfanoni k**ar su Nestle, Unilever da sauran su da su duba su gani ko akwai abin da za su iya amfani da shi wanda kasar ke nomawa a maimakon su siyo a kasashen waje.

Me za kuce akan hakan?

www.premiumtimesng.com

Want your establishment to be the top-listed Bar/pub in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Gombe