Zamfara State APC Network Awareness
Wannan shafi an buda shi ne domin wayar da kan jama'a bisa kyakkyawar manufar jam'iyyar APC da Kuma kare martabar jam'iyyar.
27/06/2021
Ga dukkan alamu baya za ta haihu. Za ta haifi 'Da, kuma 'Dan shege, kuma makaho.
Komawar Matawalle APC!!!
Muna kira ga Kwamishinan Addini na jahar Zamfara cewa kada ya yarda a sake bata mishi suna irin yadda akayi mishi bara.
05/04/2021
A cigaba da shirye-shirye da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ke yi na kutsowa cikin Jam'iyyar APC ta ko wane hali. Yau, 5/4/2021, ya gayyaci Gwamnonin Jam'iyyar APC, ciki hadda shugaban riko na Jam'iyyar APCn, Gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni, Gwwmnan jahar Kebbi, Bagudu da Gwamnan jahar Jigawa, Badaru, ya ba su cin hancin gidan masaukin baki na jahohin su, da gwamnatin jahar Zamfara ta gina mu su.
Babban abunda ya ba kowa mamaki shine irin yadda aka kammala taron cin hancin ba tare da ambata maganar WANKAN Gwamnan zuwa Jam'iyyar APC ba.
A cewar 'yan PDPn, a gobe Talata 6/4/2021 ne Gwamnan zai aiyana ficewa daga Jam'iyyar shi ta PDP zuwa Jam'iyyar APC. Wasu na ganin zuwan su Mai Mala Buni, na da alaka da ficewar Gwamnan a gobe. Zuwa yanzu da yawa cikin al'ummar Zamfara sun saki kari kan maganar WANKA da Gwamnan zaiyi a gobe.
Muna rokon Allah ya kara daukaka Jam'iyyar APC, da jagoran Jam'iyyar APC na jahar Zamfara Dr. Abdul'azez Yari Abubakar.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the organization
Website
Address
Gusau