Ckstudio
News | Entertainment | TV | Content Creator
02/05/2026
Jagoran Kwankwasiyya; Rabiu Musa Kwankwaso ya umarci magoya bayansa da su yi murabus daga jam’iyyar ADC a shirye shirye sa na Kimawa jam’iyyar NDC.
Tsohon shugaban jam’iyyar NNPP, wanda ya shiga ADC makonni kaɗan da s**a gabata, zai koma NDC tare da Peter Obi, wanda shi ma ake sa ran zai sanar da sauyawar tasa nan ba da jimawa ba. Ana kuma hasashen cewa za su tsaya takara tare a matsayin tikitin shugaban ƙasa na Obi–Kwankwaso.
Bugu da ƙari, ana sa ran dukkan ‘yan majalisar da s**a sauya sheka daga NNPP zuwa ADC za su sanar da murabus dinsu daga jam’iyyar, domin su ma za su koma NDC. Haka kuma ana tattaunawa da wasu ‘yan majalisar da s**a bi Peter Obi zuwa ADC kan wannan batu.
A halin yanzu, akwai ƙoƙarin ƙarshe da wasu shugabannin haɗin gwiwa ke yi domin dakatar da wannan sauyawar, amma da alama ba zai yi nasara ba, domin ɓangaren Kwankwaso ya yi wani zama da shugabannin NDC a daren jiya domin kammala tattaunawa kan shirin sauyawar nasu.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Tudun Wada
Gusau