Hausa Plus
HausaPlusTv. Tashar Talabijin Ta Yanar Gizo. Mai Yada Sahihan Labaran Duniya. Da Shirye Shirye Masu Fadakarwa Nishadan Tarwa. Awa Ishirin da hudu.
13/03/2026
DA DUMI DUMI: Amurka ta koka kan makudan kudade da take asara a yakin da take yi da Iran.
A ƙasa da makonni biyu da fara yakin Amurka da Iran, sojojin Amurka sun ƙone adadin makamai da ake tsammanin zai ɗauki shekaru kafin a mayar da su, musamman makaman zamani irin su Tomahawk da na kariya.
Wannan ya jefa damuwa game da ƙarin farashi da kuma rage yawan ajiyayyun makamai.
Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon na neman ƙarin dala biliyan $50 don cika gibin abin da aka rasa na ajiya, abin da ya ƙara tada muhawara a Amurka kan yawan kashe kuɗi don yaki.
Wasu ‘yan majalisa daga jam’iyyun daban-daban sun nuna damuwa cewa amfani da makamai zai iya sanya Amurka cikin rauni a hannun wasu abokan gabanta a nan gaba. 
A baya ma dai Pentagon din ta bayyana cewa, yakin ya lashe wa ƙasar Amurka Dala biliyan $11.3 a ranakun farko-farko na yakin.
゚
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Yar'aduwa Road
Gusau