Gwarzo Gida Gida Reporters

Gwarzo Gida Gida Reporters

Share

Gwarzo Local Government
Kano state

Photos from Gwarzo Gida Gida Reporters's post 03/06/2026

SANARWA GA AL'UMMAR KARAMAR HUKUMAR GWARZO

A madadin shugabannin jam'iyyar APC na Karamar Hukumar Gwarzo,
muna kira ga daukacin matasa da manya wadanda s**a kai shekarun yin zabe da su yi kokari su je su yi katin zabe (PVC).

Katin zabe shi ne mabuɗin amfani da haƙƙin ɗan ƙasa wajen zaɓen shugabanni nagari.

Duk wanda ba shi da katin zabe ba zai iya kaɗa ƙur'arsa ba a ranar zaɓe.

Haka kuma, yin rajistar katin zabe na taimakawa wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya da tabbatar da cewa muradin al'umma ya samu wakilci.

Don haka muna ƙarfafa kowa da kowa da ya cancanta da ya yi anfani da wannan dama domin makomar al'umma da ƙasarmu baki ɗaya.

Allah Ya ba mu ikon sauke nauyin da ya rataya a wuyanmu.

Hon Ibrahim Ayuba Gwarzo
Sakataran Yaɗa Labaran Jam'iyyar APC na Karamar Hukumar Gwarzo Kuma shugaban kungiyar Gwarzo Gida Gida Reporters

20/05/2026

SANARWA TA MUSAMMAN.

Amadadin Shugaban Kwamitin yada Labarai na babban taron tabbatar da Mai Girma Gwamnan jihar Kano H.E Abba Kabir Yusuf, Karkashin jagorancin Hon Musa Iliyasu Kwankwaso tareda Membobinsa.

Suna Gayyatar kafatannin Al,umar jihar Kano zuwa Babban taron tabbatar da Mai Girma Zababben Gwamnan jihar Kano a matsayin Wanda zai sake tsayawa jam’iyyar Apc ta karar kujerar Gwamna a zaben Shekara ta2027.

Wanda zai gudana a Gobe Alhamis karfe 11 na safe.
Gurin taro Babban filin wasa na Sani Abacha dake Unguwar kofar Mata.

Allah yabada ikon Halarta Ameen.

SANARWA DAGA SHUGABAN KWAMITI HON MUSA ILIYASU KWANKWASO.

Want your organization to be the top-listed Government Service in Gwarzo?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Gwarzo