Jibwis Hadejia
Shafin kungiyar izala ta karamar hukumar Hadejia, don yada da'awah, karantarwa sanarwa sada zumunci da yayata ayyukan wannan kungiya.
🕌🕌SADAƘAR FATUN LAYYAH🕌🕌
Ƙungiyar Izalah ta karamar hukumar Haɗejia ƙarƙashin Jagorancin Shugaba Sheikh Mu'az Idris Mua'az, ta kafa kwmt dazai tabbatar da nasarar tara sadakar fatun Layya, Ga kungiyar kamar yadda muka saba Zama Zakara a Duk Shekara.
Kwamatin ƙarƙashin Jagorancin sakatare na wannan ƙungiya Malam Aminu Hassan Hadejia. Na miƙa gdy ga dukkan Musulmai dake bawa wannan aiki gudummawa a kowace Shekara. Mussmman fadar maimartaba Sarkin Haɗejia Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje CON, Saboda gagaumar gudummawar su.
A bana an tsara ayyukan karɓar fatun kamar haka:
1- Dukkan Majalisai da Masallatan mu su tabbatar da karbar fata da kuma kula da sa mata gishiri kafin karɓa.
2- ƴan agaji masu kayan Sarki kaɗai aka yarda a bawa Fatu da aka tara a Majalisai da Masallatai.
3- Majalisai dake Lunguna su taimaka su kawo fatun su bakin T**i don saukin ɗauka.
4- Ana iya kawo Fata da ƙirgi kai tsaye a Babbar cibiyar Tattara fatu dake Babban Masallacin Izalah Unguwar Matsaro,Haɗejia.
5- A kula da masu Fiɗa saboda gudun asarar fatu kamar yadda aka samu hakan a bara. A samu wanda S**a iya kuma asa gishiri.
6- Akwai Risitai na gudummar Kuɗi musamman ga wanda basu samu yin layya ba. Akwai ₦100.₦500. Sai a kawo masallatai dake kusa.
Zaa iya tuntuɓar waɗannan Lambobi don karɓar Fatun Kamar haka:
07032669478
08138297994
08066001913
08063157445
07036122995
08033897966.
✒️✒️✒️✒️✒️
Abu-Humairaa
Jibwis Haɗejia
24/05/2026
24/05/2026
LOKUTAN SALLAR IDI BABBA !
Jibwis Hadejia 1447
Ana sanarda Jamaar Musulmai na Hadejia da Kewaye, in Allah ya kaimu Ranar Laraba 27/05/2026....Zaa tayar da Sallar idi kamar haka;
1- Masallacin NTA -
Sheikh Isah Abdullahi
Karfe 7:30 na Safe.
2- Masallacin Hadejia/Jamaare-
Sheikh Mu'az Idris Mu'az
Karfe 8:00 na Safe.
Allah ya amsa mana 🙏
✍️ Jibwis Hadejia.
21/01/2026
Innalillahi wa Inna Ilaihi Rajiun!
A madadin Shugabannin wannan Kungiya na Karamar Hukumar Hadejia, karkashin Jagorancin Sheikh Mu'azu Idris Muaz Muna meka sakon Taaziyyar mu ga Shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau da Dukkan 'yan uwa da Iyalai da Al'ummar Musulmai...Kan Rasuwar Babban Malamin mu Sheikh Habibu Kaura Wanda Allah yaiwa Rasuwa a Yau Laraba 21/01/2026.
Allah ya Jikan Malam ya yafe kusakurai ya bashi Aljannah, ya bamu hakuri jure wannan Rashida.
✍️ Usman Muhd Isma'il
Jibwis Social media
Chairman Hadejia.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the place of worship
Telephone
Website
Address
Hadejia
Hadejia
HJA