TASKA
News Update
10/06/2023
Godwin Emefiele baya hannunmu - DSS
Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya ta DSS ta ce yanzu haka ba ta tsare da tsohon Gwamnan Babban Banki (CBN) Godwin Emefiele.
"Yanzu haka, Emefiele ba ya tare da mu," in ji hukumar cikin wani saƙon Twitter.
Tun a daren jiya Juma'a wasu rahotanni s**a ce jami'an tsaron sun yi awon gaba da shi jim kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi daga muƙaminsa.
Ba wannan ne karon farko da rahotanni ke alaƙanta tsohon gwamnan da DSS ba, musamman tun bayan da ya ƙaddamar da shirin sauya takardun naira da kuma rage yawan garin kuɗin a hannun mutane bisa amincewar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan bankin ne nan take cikin wata sanarwa, inda aka umarce shi da ya miƙa ragamar CBN ɗin ga mataimakin gwamna mai kula da harkokin gudanarwa, Folashodun Adebisi.
Mista Adebisi zai kasance muƙaddashin gwamna har sai an kammala binciken zarge-zarge a kan Emefiele da kuma sauye-sauye a bangaren kuɗi, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
09/06/2023
President Bola Ahmed Tinubu observed Jumat at the Abuja Central Mosque alongside the Sultan of Sokoto, His Eminence, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar
17/07/2022
Ka Bar Murna Ba PDP Muka Zaba Ba, Adeleke Muka Zaba, Don Haka Kuri'armu Ta Tinubu Ce A Yayin Zaben 2023, Martanin Wasu Al'ummar Jihar Osun Ga Atiku
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Hadejia