Tarihi Daga Hadejia

Tarihi Daga Hadejia

Share

Tarihi rushin al'umma

02/01/2026

Daga cikin karamomin shehu Danfodiyo akwai sanin gaibu.

A cikin littafin karamomin shehu Usamn Danfodiyo Wanda waziri Usman Gidado ya rubuta akwai wani labarin da aka kawo na wata mata daga cikin kabilar Hausawa da ta gamu da ’yan fashi akan hanyarta daga Tuareg,
Tana tafiya ita kaɗai a tsakar daji, tana dauke da zani wanda take shirin sayarwa.
Data ga hakan sai tayi bakance ta ce a ranta: “Idan Allah Ya tseratar da ni daga waɗannan ’yan fashi, zan ɗauki tsabar kuɗi dubu uku in ba wa Shehu a matsayin kyauta.”

Yan fashin Nan s**a ce mata: “da wa kuke tafe?” sai matar Nan Ta amsa “ni da Mijina.” da s**a duba bayanta Kuma sai s**a ga wani mutum yana zuwa daga baya dauke da makami,. Sai s**a bar ta ta wuce Basu mata komai ba.

Bayan sun tafi, ta duba bayanta, sai ta ga babu kowa.

Daga nan sai ta ɗauki tsabar kuɗi dubu uku zuwa ƙauyen da Shehu yake.

da ta isa, sai ta boye dubu ɗaya a gidanta, ta ɗauki dubu biyu ta kai wa Shehu.

Ta same shi yana bada karatu a lokacin, sai fada masa labarin abin da ya faru,
Amma sai ta boye bata faɗi yawan kuɗin da ta yi alƙawarin zata baahi ba,
Sai shehu ya ce mata: “to ina dubu ɗaya da kika boye?
Sai Ta ce: “Yana gidana.” Sai ya yi murmushi ya ce: “To, ki je ki kawo mini shi!.

24/10/2025

Gwamnan Bauchi ya kirkiri masarautu masu yawa a jihar bauchi wanda ya maida yawan sarakunan jihar zuwa ashirin, daga ciki ya nada yayansa a matsayin sarki mai cikakken iko..

Allah yakyauta .

21/07/2025

Muna yiwa masu bibiyarmu fatan alkhairi.



Tarihi shine rushin kowacce al,umma..

21/07/2025

Haruna uji a wakarsa da yayi ta ta,aziyyar Gwamnan jihar Sokoto Col. Umar Muhammad Hadejia

Allah yajiqansu da rahma.. amin

21/07/2025

Haruna Uji a wakarsa ta sarkin Bai din Hadejia hakimin Guri Alhaji Muhammad Bahari,,

Allah yajiqansu da rahma..

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Hadejia?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Address


Hadejia
HADEJIACITY