Mairakumi

Mairakumi

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Mairakumi, News & Media Website, Hadejia.

Photos from Mairakumi's post 03/10/2025

ABIN KOYI: Yadda Wani Matashi Ya Kwashe Shekaru Sama Da 25 Yana Yi Wa Mahaifiyarsa Tallar 'Yar Tsala

Daga Aji Kima Hadejia

Mabo ɗan Mai Tsala matashi ne dan asalin karamar hukumar Hadejia da ya shafe sama da shekaru ashirin da biyar (25) yana taimakawa mahaifiyarsa wajen tallar tsala. Duk da cewa akwai damarmaki da dama da zai iya tsunduma cikinsu, ya zaɓi wannan sana’a saboda tarbiyya da biyayya da ya ke yiwa mahaifiyarsa.

Wannan lamari ya nuna irin darajar da ya baiwa mahaifiyarsa da kuma muhimmancin taimakon iyaye. A yau da yawa daga cikin matasa suna guje wa irin waɗannan ayyuka, suna ɗaukar su a raine. Amma Mabo ya zama abin koyi, domin ya fahimci cewa duk wata sana’a da ake yi da gaskiya da amana tana da daraja.

Abin da ya ke yi darasi ne ga sauran matasa:

(a) A taimaki iyaye domin albarkarsu ta tabbata.

(b) A yi koyi da juriya da biyayya.

A fahimci cewa ba'a raina sana'a komin kankantarta, sana’a ba laifi ba ce, illa ma hanyar samun halal da dogaro da kai.

Lamarin Mabo darasi ne da ya kamata matasa su ɗauka a matsayin izina wajen nuna kauna, biyayya da kuma taimakon iyaye.

30/09/2025

DA DUMI-DUMI: Sabon rahoto ya gargadi Najeriya kan raguwar buƙatar Mai a Duniya - An nemi ta mayar da hankali gun noma

Daga Muryoyi

Wani sabon rahoto da ƙungiyoyi Climate Strategies da Salzburg Global s**a wallafa ya bayyana cewa Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki sakamakon raguwar buƙatar mai a duniya, abin da zai iya jefa tattalin arzikin ƙasar cikin matsala.

Rahoton ya bukaci gwamnati ta mai da hankali kan fitar da kayayyakin da ba na mai ba kamar noma, masana’antu, ma’adanai da makamashi, da sauransu domin rage dogaro da mai da kuma kare ayyukan yi da kudaden shiga a nan gaba.

Muryoyi ta ruwaito rahoton, ya jaddada cewa dogaro da ƙarfin man fetur da gas yana sa Nigeria zama mai rauni yayin da kasashen duniya ke ƙara yin nisa

29/09/2025

Da dumi'dumi: Gwamnatin Tarayya ta Samu Naira Biliyan 250bn Don Gina Jirgin ƙasa mai Anfani Lantarki a Kaduna da Kano.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta samu kimanin naira biliyan 250 don gina jirgin ƙasa mai sauƙi (Light Rail) a jihohin Kaduna da Kano. Wannan shirin, a cewar gwamnati, zai taimaka wajen rage cunkoson hanyoyi da kuma inganta sufuri a Arewa maso Yamma.

Gwamnati ta ce aikin zai inganta tattalin arziki da sauƙaƙa zirga-zirga ga al’umma, musamman ma tsakanin manyan biranen nan guda biyu.

Want your business to be the top-listed Media Company in Hadejia?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Hadejia