SHUNI
Ingantattun labarai masu ɗaukar hankali—ilimantarwa, faɗakarwa, da nishadantarwa.
09/06/2026
Rahotanni daga fagen siyasar Kano na nuni da cewa jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, na ci gaba da zawarcin tsohon ɗan takarar gwamnan Kano na APC a 2023, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, domin ya koma jam’iyyar ya tsaya takarar gwamnan jihar a zaɓen 2027.
Bincike ya nuna cewa ana tattaunawa da wasu na kusa da Gawuna, inda aka ce ADC ta yi masa tayin tikitin gwamna da goyon bayan kamfen. Sai dai har yanzu babu wata sanarwa kai tsaye daga Gawuna ko shugabannin ADC da ta tabbatar da sauya sheƙar, lamarin da ya sa batun ke ci gaba da kasancewa a matakin rade-radi da tattaunawar siyasa.
Wannan na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun bayyana cewa a baya an ayyana Gawuna a matsayin ɗan takarar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya a ƙarƙashin NDC, yayin da Aminu Abdussalam Gwarzo ya fito a matsayin ɗan takarar gwamna. Idan tattaunawar ADC ta tabbata, ana ganin hakan ka iya sake sauya taswirar siyasar Kano gabanin 2027.
09/06/2026
Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress, NDC, reshen Jihar Kano, ta sauya wasu ‘yan takara da aka ce suna da alaƙa da tafiyar Kwankwasiyya, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a siyasar jihar gabanin zaɓen 2027.
Rahotanni sun nuna cewa kujerun da batun ya shafa sun haɗa da wasu na Majalisar Wakilai ta Tarayya da kuma na Majalisar Dokokin Jihar Kano. A cewar bayanan da s**a fito, jam’iyyar ta ce matakin na da alaƙa da tsarin raba mukamai na 60/40 tsakanin tsohuwar tsarin NDC da ɓangaren Kwankwasiyya, amma ɓangaren Kwankwasiyya na nuna rashin jin daɗinsa kan sauye-sauyen.
Wannan rikici na zuwa ne a daidai lokacin da Kano ke ci gaba da zama ɗaya daga cikin jihohin da ake sa ido a kai a siyasar 2027. Masu lura da al’amuran siyasa na ganin idan ba a sasanta ba, saɓanin ka iya shafar ƙarfin haɗin kan NDC da tafiyar Kwankwasiyya a jihar.
09/06/2026
INEC TA ƊAUKAKA ƘARA KAN HUKUNCE-HUKUNCEN KOTU DA S**A SHAFI JADAWALIN ZAƁEN 2027
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta bayyana cewa ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙalubalantar wasu hukuncen Kotun Tarayya da s**a shafi ikon hukumar na tsara jadawalin ayyukan babban zaɓen 2027.
Shugaban INEC, Prof. Joash O. Amupitan, SAN, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin taron tattaunawa na biyu na shekara da shugabannin jam’iyyun siyasa a hedikwatar hukumar da ke Abuja. Ya ce hukuncen kotunan sun haifar da ruɗani kan wasu muhimman matakai na shirye-shiryen zaɓe, musamman batutuwan jadawalin fidda ‘yan takara da sauran ayyukan jam’iyyu.
INEC ta yi gargaɗin cewa idan ba a samu fayyacewar shari’a cikin lokaci ba, hakan ka iya kawo cikas ga shirye-shiryen zaɓen 2027. Hukumar ta bukaci jam’iyyun siyasa su ci gaba da bin ƙa’idojin zaɓe, yayin da ake jiran hukuncin manyan kotuna kan batun.
08/06/2026
Shin Ko Kun San ?
A wasu yankuna na ƙasar Norway, musamman wuraren da suke kusa da Arctic Circle, rana kan ci gaba da haskawa har cikin dare a wasu watannin shekara. Ana kiran wannan da Midnight Sun. Wannan na faruwa ne saboda yadda duniya take karkata yayin da take zagaya rana. Saboda haka, akwai lokutan da mutane ke rayuwa ba tare da cikakken dare ba na tsawon kwanaki ko makonni.
Darasi: Duniya tana da wurare da yanayi masu ban al’ajabi fiye da yadda muke zato.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Jimeta
640101