General BMB

General BMB

Share

African Actor | Film Director | Influencer My name is Bello Mohammad Bello (General BMB)

23/06/2026

Al'ummar birane da karkara, wannan sakon naku ne baki daya, musamman ma 'yan uwanmu na karkara.

22/06/2026

Wannan mummunan lamari da ya faru ya sake tabbatar da yadda rayuwar talakan Nigeria ta rasa daraja a idon wadanda s**a fito neman kuri'unsu. An kashe mahaifiya ta hanyar kona ta da ranta saboda zargin karya, Yaranta na cikinta suna kallo abin tausayi.

Wannan rashin daukar mataki na gaggawa daga bangaren gwamnati da jami'an tsaro yana nuna halin ko-in-kula da rashin damuwa da rayuwar talakan da akayi rantsuwa za a kare. Idan har gwamnati ba za ta iya samar da tsaro da tabbatar da cewa doka ta yi aiki ba, to mene ne amfanin shugabancin?

Wadannan marayu da aka bari cikin fargaba, ba za su taba mance wannan mummunan rashin adalcin ba. MUNA KIRA GA MAHUKUNTA

Gwamnati da Jami'an Tsaro Dole ne a gudanar da bincike na gaggawa don kamo duk wanda ke da hannu a wannan kisan rashin imani.

Gwamnati da kungiyoyin kare hakkin dan adam dole su shiga tsakani don tabbatar da an ba wa wadannan yara kariya, da kuma tabbatar da makomarsu.

Ya ku 'yan uwa talakawan Najeriya, yaushe ne zukatanmu s**a bushe har muka daina tsoron Allah? Yaushe ne muka koma dabbobi da ba sa amfani da hankali?

Yau an kashe uwa a gaban yaranta saboda jita-jita da rashin bincike. Gobe murna ko bakin ciki zai iya hawa kan kowa daga cikinmu. Idan muka ci gaba da zama masu zubar da jinanen Yan uwamu, to Allah zai cire mana albarka da kwanciyar hankali gaba daya. Mu ji tsoron ranar da za mu tsaya a gaban Ubangiji don ba da bahasin jinin da muka zubar ba tare da hakki ba.

21/06/2026

Ya ALLAH 😢

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Jos?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Address


Plateau
Jos
930001