Jaridar Azurfa

Jaridar Azurfa

Share

Ingantattun labaran Afirka da duniya a tafin hannu! Babu sirki da soki burutsu

02/02/2026

FILM DIN GIDAN DUNIYA..

Ya zamanto Film mafi Shahara da Kayatarwa a cikin Finafinan da aka taba yi a Kannywood,Saboda Tsaruwarsa da kyawunsa da Aikin da Aka masa.

Masana Sun Tabbata ba a tabayin Film mai Armashin Film din Gidan Duniya ba,inda s**a bayyanashi a matsayin mafi kyawun film a Duniyar Fina-finan Hausa.

Maza Ku hanzarta ku kalli shirin gidan Duniya, Episode 3 kai tsaye Yanzun haka a Youtube Channel Link na Comment Section.👇👇👇👇

24/11/2025

DA DUMI-DUMINSA: Uwargidan Shugaban Majalisar wakilai ta biyawa Mutane 2000 kudin aikin Ido a Zariya..

Maidakin Shugaban Majalisar wakilai ta Kasa Dokta Abbass Tajuddeen wato Hajiya Fatima Abbass Tajuddeen,ta dauki Nauyin Aikin ido kyauta ga marasa galihu mutum dubu biyu ciff a babban Asibitin koyarwa na A.B.U dake tudun wada Zariya. wanda tuni an shirya fara gudanar da aikin tantance wadanda za su ci moriyar aikin.

Uwargidan Kakakin Majalisar,wacce har wa yau ke rike da Saurautar Tauraruwar Iya,ta biya wannan gagarumin aikin ne karkashin Gidauniyarta ta Fatima Tajudeen Abbas inda daga gobe za a shirya shiri na musamman domin aiki ga masu lalurar Ido, da duk wani me fama da lalurar Ido,inda kwararru a fanni lafiyar ido zasu duba al'umma.

Bayan ga duba lafiyar idon, ga wanda idansu ke bukatan aiki nan take likitoci kwararru zasu masa aiki kyauta, haka ga wanda idan ke bukatan Tabarau (Eye Glasses) shima za a samar masa dai dai da yanda idansa ke bukata.

Wannan bashi ne karon farko ba da maidakin Shugaban Majalisar Wakilai ta Ƙasa Hajiya Fatima Abbas Tajudeen ke shirya irin wannan shiri domin kyautatawa Al'umma ba. watannin baya ta shirya gagarumin shirin koyar da sana'oi ga mata da matasa inda kowannensu ya rabauta da Jarin Naira Dubu Hamsin 50k.

Za a shafe kwanaki 5 ne dai ana tantance Mutane kafin fara gudanar da Aikin wanda shine irinsa na farko da za a duba dubunnan mutane kuma a musu aiki kyauta a Zariya. dama ce ga al'umman Zaria dama makofta akan su fito gobe ganin yanda harkan lafiyar ido tayi tsada, wannan shiri tinda ga farkonsa har karshe kyauta ne ba a bukatan komai daga mare lafiya.

Daga Saifullahi Lawal Imam.

09/05/2025

Jumma'atu

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kaduna?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Kaduna