AMANA PRESS

AMANA PRESS

Share

An samar da wannan kafar ce domin bayar da labarai kamar yadda suke ba tare da nuna wani bambanci ko son rai ba. Haka ma muna fassara wato Translation.

30/05/2026

Tsohon Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Dawakin Kudu Da Warawa Mustapha Bala Dawaki Ya Canza Sheka Daga Jam'iyyar APC Zuwa NDC

Yayin da babban zaben kasa na shekarar 2027 ke kara kusantowa, shugaban ma'aikata na helkwatar jam'iyyar APC ta kasa (Chief of Staff), kuma tsohon dan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Dawakin kudu da Warawa a jihar Kano, kuma dan takarar komawa majalisar a kakar zabe ta 2027, Alhaji Mustapha Bala Dawaki ya canza sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar NDC ta su Injiniya Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso.

Canjin shekar ta sa ya biyo bayan zargin rashin adalci da shi da magoya bayansa ke yi, dangane kwarfiya da aka yi musu yayin zaman sulhu da jam'iyyar ta yi na fidda 'yan takarkarun majalisun jiha dana tarayya karkashin jagorancin Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Hakan nan zaben fidda gwani na wanda zai tsayawa jam'iyyar takarar dan majalisar tarayyar na kato bayan kato da aka gabatar a kafatanin mazabun kananan hukumomin Dawakin kudu da Warawa, bayan rashin samun daidaito tsakanin 'yan takarkarun, wanda aka baiwa dan majalisar jiha mai ci a yanzu, Alhaji Shu'aibu Rabi'u Nagoggo Gano nasara ya bar baya da kura, inda magoya bayan Mustapha Bala Dawaki su kai zargin an tafka magudi yayin tattara kuru'un da aka kada a zaben.

Tuni dai dimbin magoya bayan tsohon dan majalisar tarayyar ke bayyana ficewarsu daga tsohuwar jam'iyyar ta sa ta APC a fili, ta hanyar aikawa da sakonni a shafukan sada zumunta na zamani, da kuma nuna sabon katin shaidarsu na shiga jam'iyyar NDC da s**a mallaka.

20/05/2026

Ga gaskiya abin da ya faru a Fagge ta Jihar Kano

SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR FAGGE HON SALISU USUMAN MASU, KENAN YAYIN GUDANAR DA TABBATAR DA ZABEN FIDDA GWANI NA DAN MAJALISAR JAHA HON TUKUR MUHAMMAD.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kaduna?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


Kaduna