FCT
Free Browsing, Business Centre & Bookshop
LARABA, 11 GA MARIS
NASSI: JOEL 2:21-32
KAN MAGANA: SHAFEWA TA MUSAMMAN
Anabcin Joel ya gangara har zuwa zamanin karshe wanda
muke ciki. Ya fara lokacin pentikost, lokacin da manzo Bitrus
ya fada cewa zubowar Ruhu Mai Tsarki cikan anabcin annabi
Joel ne (A. Manzani 2:16-17).
Saboda haka muna rayuwa a lokacin da mutanen Allah na
samun shafewa ta musamman da ikon Ruhu Mai Tsarki domin
aikata manya manyan abubuwa na bishara.
Duk abinda muke bukata mu yi shine mu roki Allah cikin
addu'a muna kuma bada gaskiya.
Daga tarihin Ducan Campbell, wani mutum da Allah ya yi
amfani da shi sosai domin farfadowa a Britain, sai da muryar
wannan bawan Ubangiji ta dushe, ta bata gaba daya, amma
daga baya Allah cikin ikonsa ya warkad da shi.
Nan danan ya warke, bisa ga wurin da muka karanta yau,
Campbell shi ma ya yi addu'a cewa Allah ya maida mashi
shekarun da s**a salwanta; da fari s**a cenye.
Allah kuwa ya amsa mishi ta wurin shafe shi da ikon Ruhu Mai
Tsarki sosai, aka sami falkawa, ceton da mutane s**a samu
ya zama fiye da na sauran shekarun baya da ya yi na aikin
bishara.
TAMBAYA:
Kana bukatar shafewa ta musamman na Ruhu
Mai Tsarki?
ADDU'A:
Ya Ubangiji, in ka yarda ka shafe ni da iko na
musamman na Ruhu Mai Tsarki domin in sake samun
abubuwan da na rasa a shekarun baya da fari s**a cinye mini,
a cikin sunan Yesu, Amin.
ABINCIN YINI 2020.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Contact the place of worship
Telephone
Website
Address
Lugbe
Kaduna