Global Community For Human Rights Network

Global Community For Human Rights Network

Share

we're all Equal Before the Law. The law is the same for everyone, it must treat us all fairly

20/03/2026

🌙✨ SAKON TAYA MURNAR SALLAH ✨

GLOBAL COMMUNITY FOR HUMAN RIGHTS NETWORK (GCHN)

Na taya daukacin al’ummar Musulmi murnar Babbar Sallah.
Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya gafarta mana zunubanmu,
Ya maida mana ita cikin ƙoshin lafiya, zaman lafiya da wadata.

Muna kira ga al’umma da su kasance masu haƙuri, tausayi, da haɗin kai,

tare da mutunta haƙƙin ɗan Adam a kowane lokaci.

🤲 Allah Ya kawo mana ƙarshen matsalolin tsaro,

Ya ba mu zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya da duniya baki ɗaya.

🌍 Global Community for Human Rights Network (GCHN)

“Muryar Kare Haƙƙin Dan Adam”

14/03/2026

Global community for human rights network Ungogo branch,

Hujjojin Doka Kan Kare Haƙƙin Wanda Aka K**a a Najeriya.

1. Hana Azabtarwa ko Dukar Mutum (Prohibition of Torture)
A karkashin Section 34(1)(a) na Constitution of the Federal Republic of Nigeria, an tabbatar da cewa kowane mutum yana da haƙƙin mutunci da daraja, kuma:
“No person shall be subjected to torture or to inhuman or degrading treatment.”
Haka kuma Section 2 da Section 8 na Anti-Torture Act sun haramta duk wani nau’i na:
azabtarwa
duka
wulakanci
ko tilasta mutum ya amsa laifi.
Duk jami’in tsaro da ya aikata haka yana iya fuskantar hukunci a kotu.

2. Hana Cin Zarafi ko Wulakanta Mutum
A karkashin Section 34(1) na Constitution of the Federal Republic of Nigeria, doka ta tabbatar da Right to Dignity of Human Person.
Wannan yana nufin:
ba a yarda jami’in tsaro ya zagi mutum ba
ko ya wulakanta shi yayin bincike ko tsarewa.

3. Haramcin Tilasta Mutum Ya Amsa Laifi
Section 35(2) na Constitution of the Federal Republic of Nigeria ya ba wanda ake zargi damar:
yin shiru
neman lauya kafin bada bayani.
Wannan yana nufin ba a yarda jami’an tsaro su:
tilasta mutum ya amsa laifi
ko su tilasta masa bada shaida a kansa.

4. Haramcin Tilasta Sa Hannu a Bayani
A karkashin Section 29(2) na Evidence Act:
Duk wani confessional statement da aka samu ta hanyar tsoro, barazana, ko azabtarwa ba zai karɓu a kotu ba.
Saboda haka:
idan an tilasta mutum ya sa hannu
ko aka azabtar da shi kafin ya bada bayani
to wannan bayanin ba zai zama hujja a kotu ba.

5. Haramcin Tsare Mutum Ba Tare da Kai Shi Kotu ba
Section 35(4) da 35(5) na Constitution of the Federal Republic of Nigeria sun bayyana cewa:
Mutumin da aka k**a dole ne a kai shi gaban kotu cikin:
awa 24 idan kotu tana kusa
ko awa 48 idan kotu tana nesa.
Idan ba a yi haka ba, tsarewar tana zama illegal detention.

6. Haramcin K**a Mutum Saboda Laifin Wani
Section 36(5) na Constitution of the Federal Republic of Nigeria ya kafa ka’idar:
“Every person who is charged with a criminal offence shall be presumed to be innocent until he is proved guilty.”
Saboda haka:
ba a k**a mutum saboda laifin ɗan uwansa ko abokinsa ba
sai idan akwai hujjar cewa shi ma yana da hannu a laifin.

7. Haramcin Kwace Dukiyar Mutum Ba Tare da Doka ba
Section 44(1) na Constitution of the Federal Republic of Nigeria ya tabbatar da Right to Property.
Wannan yana nufin:
ba a kwace waya, kudi, ko wata dukiya ba
sai da izinin doka ko kotu.

8. Haramcin Karɓar Rashawa (Bribery)
A karkashin Section 98 na Criminal Code Act:
duk wani jami’in gwamnati da ya karɓi:
kudi
kyauta
ko wata fa’ida
domin yin wani aiki ba bisa doka ba, yana aikata laifin rashawa (bribery).

9. Barazana da Makami Domin Tilasta Bayani
Section 2 na Anti-Torture Act ya bayyana cewa:
barazana, tsoratarwa, ko amfani da makami domin tilasta mutum ya bada bayani ana ɗaukarsa torture.

10. Haƙƙin Ganin Lauya da Sadarwa da Iyali
A karkashin:
Section 35(2) na Constitution of the Federal Republic of Nigeria
Section 6(2) na Administration of Criminal Justice Act
mutumin da aka k**a yana da haƙƙin:
ganin lauya
sadarwa da iyalansa ko abokansa.

C,O Ungogo Branch Sabi'u Auwal gama.

23/02/2026

🚨 KU KARANTA KU YADA KU NEMI ADALCI!

GLOBAL COMMUNITY FOR HUMAN RIGHTS NETWORK NIGERIA

tana Allah wadai da kakkausar murya kan kin bin umarnin kotu da Hukumar Department of State Services (DSS)

tayi na kin maida Walida ga iyayenta

tun bayan zargin yin garkuwa da ita da wani jami’in DSS yayi.

❗ Wannan lamari ba wai take hakkin mutum daya bane kawai

barazana ce ga ‘yancin kowane dan kasa.

⚖️ Idan ba a mutunta kotu ba, wace doka za ta kare talaka?

Idan aka raba ‘ya da iyayenta, wa zai ji dadin wannan zalunci?

Shiru ba mafita bane adalci dole ne!

Muna kira cikin gaggawa ga duk masu ruwa da tsaki:

A gaggauta bin umarnin kotu

A mayar da Walida ga iyayenta ba tare da bata lokaci ba.

A hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan lamari

jinkiri, adalci hanawa ne!

Ka/ki yada wannan sako domin duniya ta sani

Muna yabawa fitaccan dan jarida
Abubakar haruna galadanci

bisa aiki tukuru dan neman anyi adalci a wanna cinzarafin da akayiwa Walida da iyayanta wanna shine aiki jarida



GLOBAL COMMUNITY FOR HUMAN RIGHTS NETWORK NIGERIA

Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Kano
700001