GSN Hausa

GSN Hausa

Share

Ziyarci GSN Hausa don labarai ingantattu daga Najeriya, Nijar, Kamaru da Ghana, tare da sauran duniya baki daya. Kada ka manta da LIKE da FOLLOW. Mungode!

02/02/2026

RAYUWA KENAN! Innalillahi wa Inna ilaihi raaji'un!

Allah Ya yi wa shahararren malamin addinin Muslunci, Sheikh Usman Kusfa Zariya, wanda aka fi sani da Rigi-Rigi, rasuwa a daren ranar Lahadi 1 ga Fuburairun 2026, kamar yadda majiyoyi na kusa da ahalin s**a tabbatar.

Sheikh Usman Kusfa, wanda ya shahara a kafafen sada zumunta saboda salon wa’azinsa, ana sa ran za a gudanar da jana’izarsa a yau Litinin, a gidansa da ke Zariya.

24/01/2026

An tsinci jariri sabuwar haihuwa a Tudun Murtala, Kano — lamarin ya tayar da hankalin jama’a.

An tsinci jariri sabuwar haihuwa a safiyar yau a yankin Tudun Murtala, kusa da makabarta da ke cikin birnin Kano.

Wata mazauniyar yankin, Ummulkhair Ayuba Musa, ta shaida wa Freedom Radio Nigeria cewa sun wayi gari da ganin wani abu a nannade cikin leda a gefen makabartar. Bayan an duba abin, sai aka gano jariri ne mace, sabuwar haihuwa.

Rahotanni sun nuna cewa har yanzu ba a yi mata cikakken kulawar haihuwa ba, lamarin da ya nuna jaririyar ta zo duniya ne a cikin yanayi mai tayar da hankali.

A halin yanzu, ana sa ran za a yi mata sallah a binne ta kamar yadda addini ya tanada.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Tudun Wada, Nassarawa
Kano
700282