Limamin G-R-A

Limamin G-R-A

Share

Barka da zuwa offficial page ɗin ƴaƴan masu kuɗi na (Yusuf Musa Bin Baz) Addini cikin hikima. Kalamai masu taɓa zuciya. Ilimi. Faɗakarwa. Nishaɗi. Danna Follow ☀️

11/12/2023

ALJAMI'U LI'IBADATILLAHI WAHDAHU {1}

Halƙa ta Farko “1”

Wannan risāla me suna a sama itama risala ce daga cikin rasā'il na Allama Fadeelatu Sheikh Muhammad bin Abdulwahab rahamatullahi alaihi. Alhamdulillahi gata dai ƙarama a yawan shafuka! Amma kāfí ce wajan isar da saƙo kuma shāmila ce saboda ɗimbin ilimomin da ta ɗēbo! Allah kaɗai nake roƙo ya amfanar da mu Musamman mu ƙananun ɗalibai da abinda ke cikin ta.

الرسالة السابعة الأصل الجامع لعبادة الله وحده

بسم الله الرحمن الرحيم

فإن قيل: فما الجامع لعبادة الله وحده؟ قلت: طاعته بامتثال أوامره واجتناب نواهيه.

Malam Yace idan aka ce mene ya tattaro bautar Allah madaukakin sarki ? Ni Muhammad bin Abdulwahab sai nace yi masa biyayya ta hanyar aikata umarninsa da nisantar abinda yai hani ne.
______
{{Wannan shine: saboda haka ba komai bane cikin bautar Allah sai umartuwa da umarninsa da hanuwa da hanawarsa! Duk abinda Allah ya umarce ka da shi to haka Allah yake so ayi! a matsayin ka na bawa baka da zaɓi akai.}}

{Shi yasa ka kalli sunan risālar! الجامع لعبادة الله وحده Ma'ana abinda ya tattaro bautar Allah maɗaukakin sarki.}

فإن قيل: فما أنواع العبادة التي لا تصلح إلا لله تالى؟ قلت: من أنواعها: الدعاء والاستعانة ١ والاستغاثة، وذبح القربان، والنذر، والخوف، والرجاء، والتوكل، والإنابة، والمحبة، والخشية، والرغبة والرهبة، والتأله، والركوع، والسجود، والخشوع، والتذلل، والتعظيم الذي هو من خصائص الإلهية.

Malam Yace idan aka ce mene Nau'ikan bauta wadda ba yadda za'ayi bauta ta yi wu sai da su? Sai nace na daga ciki akwai Addu'a!

{Wanda ita dama addu'a Allah har cewa yai duk wanda yai girman kai wajan barin kiran Ubangijinsa sai ya shirgar da shi wutar jahannama yana ƙasƙantacce! duba suratu Ghāfir}.

Malam Yaci gaba da cewa Akwai Neman taimakon Allah {Wannan yana Magana ne cikin abinda ba wanda yake da iko kansa sai Allah} Akwai neman ce! {shima cikin abinda ba wanda yake da ikonsa sai Allah! Misali k**ar neman ceton da za'ai ranar alƙiyama! kaga bame iko kan haka sai Allah}.
_______
Da yanka { shima dan samun kusanci ga Allah} da bakance! {Shine kaiwa Allah alƙawarin in kaza ya same ka za kai kaza ko za kai azumi ko wani abu da yai k**a da haka! duka wannan nau'i ne na bauta}.

Da jin tsoron Allah maɗaukakin sarki! {Ma'ana irin tsoron da babu wanda za'ai wa shi sai Allah} da fatan haɗuwa da Allah da fatan abinda ke gurinsa na ni'ima, da tawakkali ga Allah {shine ka miƙa lamarinka gaba ɗaya gare shi shine zai juya komai}.

Da komawa gare shi {Saboda sama da ƙasa babu me yi maka sai shi ɗin} da yin soyayya dan shi! {dan Anan ake ƙulla Alwalā'u walbarā} da jin tsoronsa, da tsoron abinda ke gurin sa na azaba da fatan abunda ke gurinsa na aljanna, da kaɗai ta shi da bauta, da yin ruku'u dan shi, da yin sujjada dan shi, da nutsuwa dan shi, da ƙasƙantar da kai ga Allah {ma'ana ka nuna kai ba kowa bane} da girmama shi wanda hakan yana daga cikin ƙeɓantattun abubuwa na bautar Allah.

ودليل الدعاء قوله تعالى: {وَأَنَّ الْمَسَاجِدَ لِلَّهِ فَلا تَدْعُو مَعَ اللَّهِ أَحَداً} ٢

Dalili kan addu'a faɗin Allah maɗaukakin sarki inda yace “Dukkan guraben bauta na Allah ne kada ku kira wani tare da Allah” Suratu Jinni.
_______
Kamar yadda AL'IMĀMUL BAGĀWIY Ya kawo cikin Tafsirinsa yace gaɓɓan da ake nufi anan sune Tafukan hannu guda biyu! guiwa guda biyu! yatsu biyu na ƙarshen ƙafa! Sai kuma Goshi da Hanci a haɗe! idan ka lissafa bakwai kenan.

وقوله تعالى: {لَهُ دَعْوَةُ الْحَقِّ وَالَّذِينَ يَدْعُونَ مِنْ دُونِهِ لا يَسْتَجِيبُونَ لَهُمْ بِشَيْءٍ} ٣ إلى قوله: {وَمَا دُعَاءُ الْكَافِرِينَ إِلاَّ فِي ضَلالٍ} ٤.

Malam Yace Da kuma faɗin Allah maɗaukakin sarki inda Yace “ Gare shi kira na gaskiya yake! wanda suke kira ba shi ba ba zai iya amsa musu kiran nasu da komai ba” har inda Allah yake cewa “Addu'ar kafirai bata kasance ba face ɓata” Suratu Ra'ad.
_________
AL'IMÃMUL BAGAWIY YACE {لَهُ دَعْوَةُ الْحَقِّ ana nufin Tauhidi k**ar yadda ya kawo daga Aliyu bin Abi ɗalib. Abdullahi ɗan Abbas kuma yace ana nufin kalma لا إله إلا الله. Wasu malaman s**a ce ana nufin tsarkake bauta ga Allah maɗaukakin sarki. {A takaice dai in ka duba duka fassarorin suna shiga ciki}.

Har yaje ƙarshen ayar inda Yace «وما دعاء الكافرين» عبادتهم الأصنام أو حقيقة الدعاء «إلا في ضلال» ضياع Ma'ana bautar da kafirai sukewa Gumaka/ko kiran da suke musu kira na haƙiƙa! To hakan be kasance ba face ɓata/Hasara k**ar yadda yazo Cikin Tafsirul Jalalāini.
_________
ودليل الاستعانة قوله تعالى {إياك نعبد وإياك نستعين}

Malam Yace Dalili kan neman taimako {cikin abinda ba wanda yake da iko kansa sai Allah} ga faɗin Allah maɗaukakin sarki nan “Gare ka muke bauta Gare ka muke neman Taimako”

Jalãluddín Almuhallā da Jalāluddín Assuyúɗí s**a ce cikin TAFSIRUL JALĀLAÍNI Ma'ana muna keɓance ka da bauta da Tauhidi da mak**antan haka! Muna kuma neman taimakon ka cikin bautar da waninta. {Kaga kenan sauran lamurran duniya zasu shiga ciki wajan neman taimakon nasa}.
________
Saboda haka Ni me rubutu nake cewa wannan Gaɓa ce me matuƙar muhimmanci mu kula da ita ba'a neman taimakon kowa wajan abinda bashi da iko sai Allah! Saboda aikata hakan shirka ne wa lamarin Allah! Allah ya shiryar da Mu.

Yusuf Musa Bin Baz

11-12-2023.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Kumbotso Road
Kano