Inter mian
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Inter mian, Grocers, nigeria kano, Kano.
14/11/2025
JOSÉ MOURINHO YA CE:
“Na taɓa yin aiki da wasu Captain da ba shugabanni ba ne. Amma akwai ɗaya a Porto, Jorge Costa.
Ranar da ba zan taɓa mantawa ba, muna buga wasa da ƙungiyar Belenenses, kuma an doke mu 2-0 a rabin lokaci. Ina tafiya zuwa ɗakin canza kaya, kowa ya ga fushina ya kai kololuwa.
Da zan shige ɗakin sai Jorge Costa ya dakatar da ni, ya ce, ‘Malam, don Allah ka tsaya a waje na minti biyu.’ Ya shiga, ya rufe ƙofa, ya yi dukan abin da zan yi da kaina. Ya yi masifa, ya jefa musu zafi, ya tayar da hankalinsu kamar yadda na saba yi. Bayan ya gama, sai ya buɗe ƙofa ya ce, ‘Yanzu malan, shigo ka koyar da mu.’
Mun koma filin wasa, muka yi abin mamaki — muka ci 3-2. Shi kuwa, Jorge Costa ɗanfan tsakiya ne wanda ba ya cin ƙwallo; amma a wannan rana shi kaɗai ya zura biyu! Wannan shi ne bambanci tsakanin ‘cibiyi’ da ‘shugaba’. Banda cewa kana da bandeji a hannu zai sa ka zama jagora.
Jagoranci ba a siya. Ba a ƙera shi. Idan kana da shi cikin tawagarka, to ka riga ka ɗauki mataki guda gaba.”
Wafiyya Hausa
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Nigeria Kano
Kano