R.T.D YOUTH Development
Wannan feji na Aikin yada bayanan cigaban wannan kungiya
21/01/2025
Press Release
Al'ummar Garin Jujin Gobirawa Unguwar Mahauta sun yabawa Shugaban Kungiyar Cigaban Matasa na Rimin Gado Tofa Dawakin Tofa Alhaji Mudassir Adam Danshayi kuma Shugaban Gidauniyar Sahibul Hubbi abisa rawar da yake takawa wajen samar da cigaban yankin Karamar Hukumar Rimin Gado.
Malam Abdu Isa Jujin Gobirawa Unguwar Mahauta ne ya bayyyana hakan a lokacin da s**a ziyarci Shugaban o ofishinsa.
Sun kuma jaddadada goyon bayansu ga manufofi da Tsare-Tsaren Shugaban.
Da yake nasa Jawabin, Alhaji Mudassir Adam Danshayi ya tabbatarwa da al'ummar Garin Jujin Gobirawa Unguwar Mahauta cewa zai cigaba da bada fifiko wajen ganin sun samu yanayi mai kyau na cigaban yankin.
Ya Kuma gode musu abisa ziyarar tare da basu goyon baya domin cimma abinda aka sanya a gaba.
Zai Kuma dauki duba lafiyar idanun daya daga cikin mutanen Unguwar Mahauta abisa yanar Ido dake damunsa.
Haka zalika, Shugaban ya karbi bakuncin matasa daga Mazabar Yalwan Danzial a ofishinsa, da yake Jawabinsa na maraba agare su, Shugaban yaja hankalin su wajen dogaro da kai da barin kazamar Siyasa da banbadanci.
Ya kuma yaba musu tare da kara rokon su wajen haduwa guri guda domin kawowa yankin cigaba.
Da suke Jawabansu matasan sun yabawa Shugaban abisa kulawar sa da mutuntasu da yayi wajen basu lokaci domin tattaunawa da shi.
Sun kuma jaddadada goyon bayansu agare shi da kuma bukatar ganin an farfado da ayyukan da Kungiyar take aiwatarwa zuwa wasu fannoni masu mahimmanci.
Alhaji Mudassir Adam Danshayi
Chairman Rimin Gado Tofa Dawakin Tofa Youth Development founder na Sahibul Hubbi Foundation.
08/12/2024
08/12/2024
_Burina Shine Al'umma su samu Cigaba domin dorewar zaman lafiya._
Al’ummar Jujin Gobirawa Unguwar Mahauta da ke karamar Hukumar Rimin Gado a Jihar Kano, sun nuna jin dadinsu ga Alhaji Mudassir Adam Danshayi, Shugaban Kungiyar Cigaban Matasan Rimin Gado/Tofa/Dawakin Tofa, bisa sadaukarwar da yake yi na ci gaban al’ummarsu.
A ganawar da s**a yi da Shugaban kungiyar, karkashin jagorancin Malam Audu na Babale, al’ummar sun bukaci Shugaban Kungiyar Daya shige musu gaba izuwa Gwamnatin Jiha da Karamar Hukumar Rimin Gado wajen a tallafa musu wajen magance rushewar gidajensu a lokacin damina, da gina musu guraben ajujuwa na makarantun firamare da Islamiyya, da kuma kaura daga mahallin da suke ciki.
Sun yi nuni da cewa al’ummar yankin sun kai dubu daya, inda suke da gidaje kusan dari da hamsin.
Hakazalika sun kara da cewa irin wadannan kungiyoyi sune wadanda Gwamnati ya kamata ta hada hannu dasu ba.
Da yake mayar da martani, Alhaji Mudassir Adam Danshayi ya jajanta musu halin da suke ciki tare da tabbatar musu da aniyarsa ta warware matsalolin da kuma shige musu gaba wajen cimma abinda aka sanya a gaba.
Ya yi alkawarin bayar da shawarwari ga gwamnati da kuma neman tallafi daga kungiyoyi masu zaman kansu don rage matsalolin da al'umma ke fuskanta.
Shugaban kungiyar Alhaji Mudassir Adam Danshayi ya kuma bukaci al’umma da su cigaba da yiwa shugabanin kasa, jaha, da kananan hukumomi addu’a domin samun dorewar zaman lafiya da cigaban yankin.
Ya Kuma bukace su dasu kasance masu hakuri da juriya a duk halin da s**a tsinci kansu.
Alhaji Mudassir Adam Danshayi
Chairman Rimin Gado/Tofa/Dawakin Tofa Youth Development.
18/11/2024
Shugaban Kungiyar Cigaban Matasa na Rimin Gado/Tofa/Dawakin Tofa Ya Yaba da Shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na Gina Ajujuwa na Sikandire a Garin Danshayi.
Shugaban Kungiyar Cigaban Matasa na Rimin Gado/Tofa/Dawakin Tofa, Alhaji Mudassir Adam Danshayi, ya bayyana godiyarsa mai zurfi ga Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa umarninsa na gina wani block ɗin ajujuwa a garin Danshayi,mazabar Karofin Yashi, karamar hukumar Rimin Gado.
Da yake bayyana wannan mataki a matsayin babbar hanya ta inganta ilimi da kuma kawo cigaban da zai dore a yankin, Alhaji Mudassir Adam Danshayi ya yaba da jajircewar Gwamna wajen inganta rayuwar al’ummar yankin.
Haka kuma, Shugaban ya miƙa godiyarsa ga gidan Rediyon Premier bisa rahoton da s**a bayar kan kokarin wata mace mai kishin ilimi da ta shafe sama da shekaru ashirin tana koyar da mata da marasa galihu a garin Danshayi domin Cigaban al’umma.
A cikin jawabinsa, Alhaji Mudassir Adam Danshayi ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Rimin Gado da su goyi bayan wannan baiwar Allah domin cimma burinta.
Ya kuma tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da tallafa mata da sauran mutane domin cigaba da wannan aikin alheri na koyar da mata da waɗanda ba za su iya biyan kuɗin makaranta ba.
Alhaji Mudassir Adam Danshayi
Shugaba
Kungiyar Raya Matasa na Rimin Gado/Tofa/Dawakin Tofa
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Kano
Opening Hours
| Saturday | 09:00 - 12:00 |
| Sunday | 09:00 - 12:00 |