Ibrahim Abdullahi

Ibrahim Abdullahi

Share

I'm a membar at kannywood
C O E OF FIKIRA MULTIMEDIA
DIRECTOR
PRODUCER
BUSINESS MAN
TEACHER JASS

13/07/2025

Innalillahi wa innailaihir rajuon Allah ya yi wa Baba rasuwa! 🥲

10/06/2025

Allah kara lfy Baba Ado
ubangiji yakiyaye gaba

22/05/2025

Yadda na roƙi Yar’Adua kada ya yi fada da Obasanjo – Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana yadda ya roƙi marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua kada ya shiga rikici da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo.

A shafuka na 257 da 258 na tarihin rayuwarsa da ya rubuta mai suna “Being True To Myself”, wanda aka gabatar wa jama’a a ranar 13 ga Mayu, 2025, Lamido ya bayyana wasu abubuwa biyu da s**a ba shi tabbacin cewa akwai rikici tsakanin Yar’Adua da Obasanjo.

Batun Naira biliyan $16 na NIPP

Lamido ya ce ya fara zargin hakan ne lokacin da aka fara tattaunawa a Majalisar Wakilai kan shirin samar da wutar lantarki na National Integrated Power Project (NIPP) da aka kashe fiye da dala biliyan $16.

Ya ce:

> “Idan dan adawa ne ya jagoranci wannan muhawara a Majalisar, hakan zai iya zama da sauki. Amma abin mamaki shi ne, wani babban ɗan jam’iyyar PDP daga Jihar Katsina kuma aminin Shugaba Yar’Adua ne ya jagoranci lamarin.
“Ana ba da hoton cewa Obasanjo ne ya wawuri kuɗin, kuma an bar ayyukan a cikin daji. Duk da haka, daga baya abubuwa sun sha bamban.”

Lamido ya ce ya garzaya wajen Shugaba Yar’Adua domin sanar da shi, amma Yar’Adua ya ce:

> “‘Wannan batu ne da wata madasar gwamnati mai cin gashin kanta ke tattaunawa kai.’”

Kirar daga CSO Tilde

Lamido ya ce abin da ya fi daukar hankalinsa shi ne lokacin da Tilde, jami’in tsaro na fadar shugaban kasa (CSO), ya kira shi a lokacin yana ofis a Dutse.

> “Da na ɗaga waya, sai Tilde ya tambaye ni ina nake, na ce masa kawai, ‘Ina babban garina Dutse’.
“Amma abin mamaki sai ya ce, ‘Na yi zaton kana Ota tare da shugaban ka’ – sai na saki baki. Bayan na dawo hayyacina, sai na zazzaga masa zagi iri-iri, na kuma ce zan kai kara wurin Shugaban Ƙasa.
“Don lallashi sai ya ce, ‘Don Allah ku gafarce ni, na kira ne kawai don in shaida maka cewa an aiko da koke a kanka zuwa ga Shugaban Ƙasa, kuma ina da ikon dakatar da binciken.’”

Lamido ya ce bai sauko ba, sai ya ce masa:

> “Wa kake tsammanin zaka yi wa barazana? Je ka lahira!”

Ganawa da Yar’Adua a Villa

Bayan haka, Lamido ya ce ya ɗauki jirgi ya wuce kai tsaye fadar shugaban ƙasa. Ya shiga ofishin Tilde, ya kuma zazzaga masa zagi a gaban kowa.
Daga nan ya hau sama ya shiga ofishin Shugaba Yar’Adua.

Yar’Adua ya tambaye shi:

> “‘Sule, me ke damunka haka?’”

Lamido ya ce cikin rudani da fargaba, ya kusa durƙusawa, yana cewa:

> “‘Don Allah, kada ka yi fada da Obasanjo. Kai mutum ne mai asali da daraja daga gida mai mutunci. A cikin addininmu da al’adunmu, bai dace mu nuna halin rashin godiya ba ga wanda ya tsaya mana a lokacin bukata. Obasanjo ne ya tsaya maka har ka zama Shugaban Ƙasa.’”

Yar’Adua ya ce masa:

> “‘Sule, ka zauna ka nutsu.’” Sai ya kira ADC ɗinsa, Laftanar Kanal Mustapha.

Yar’Adua ya tambayi ADC ɗin:

> “‘Menene umarnina game da Obasanjo?’”
ADC ɗin ya ce:
“‘Ka ce in amince da duk wani bukatarsa, ko a cikin gida ko wajen ƙasa, ba tare da sai an nemi amincewarka ba.’”

Daga nan Yar’Adua ya ce masa:

> “‘Sule, yanzu ka huta?’”
Lamido ya ce:
“‘Na huta, Ranka ya dade,’” sannan ya yi sallama ya tafi.

02/09/2024

With mama hajjo

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Kano