Taskar Nishadi
Tashar dake baku nishaɗi ba kakkautawa
01/04/2026
Tsohon dan takarar gwamnan Kano kuma dan jam'iyyar ADC a yanzu, Salihu Tanko Yakasai, ya kalubalanci zargin cewa shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na kokarin mayar da Kano jiha mai jam’iyya daya ta hanyar dabarun siyasa.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Yakasai ya ce wannan fahimta kuskure ce, yana mai jaddada cewa Kano ba ta taba zama jiha mai jam’iyya daya ba tun daga zamanin NEPU har zuwa lokacin Santsi da Tabo, acewarsa Kano ba irin Lagos ba ce.
Ya ci gaba da cewa al’ummar Kano sun ginu ne kan siyasar kishin al’umma da tsayawa akan gaskiya, wanda ya danganta hakan da koyarwar MalamvAminu Kano.
Salihu Tanko, ya soki yadda aka rika karkatar da aiyukan raya kasa da nade-naden manyan mukaman gwamnatin ga wata Kabila guda daya, inda ya ce me aka yi wa Kano da zaisa Tinubu yayi tunanin kowa sai ya goyi bayansa?.
A cewarsa, biyayya ga shugabanci na samuwa ne ta hanyar adalci da kyautatawa, ba ta hanyar dabaru ko tilasci ba.
Yakasai ya yi gargadin cewa idan aka ci gaba da watsi da bukatun al’ummar Kano, za su mayar da martani ne ta hanyar akwatin zabe.
23/03/2026
Matashi a tafiyar Kwankwasiyya, Alh. Musbahu Baffa, da ake kira da Na Yar Talla, ya ce akwai rashin hankali da rashin tunani kayi tunanin wani zai rike maka amana, a daidai lokacin da kai kaci amanar wanda ya amince maka.
Shin ko me matashin yake nufi?
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano